Sakataren kungiyar Arewa ta ACF ya yi mutuwar fuju’a | Aminiya

Sakataren kungiyar Arewa ta ACF ya yi mutuwar fuju’a

    Maryam Ahmadu-Suka, Kaduna da Sagir Kano Saleh

Sakataren Gudanarwar Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Alhaji Mohammed Sani Soba, ya kwanta dama.

Alhaji Mohammed Sani Soba ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a ranar Asabar, 4 ga Satumba, 2021.

Sakataren Yada Labaran ACF, Emmanuel Yawe, ya tababtar a ranar Talata cewa, “Rasuwar ta kada mu matuka a ACF, inda ya shafe shekaru yana aiki har zuwa lokacin rasuwarsa.”

Ya bayyana mamacin da cewa mutumin kirki ne da ya hidimta wa kungiyar ta ACF a matsayin Sakataren Gudanarwa.

Mamacin tsohon Babban Sakatare ne a Gwamnatin Jihar Kaduna, bayan ya yi ritaya ya kama aiki da ACF a matsayin kwantaragi.

Sanarwar rasuwar da ACF ta fitar ta ce, “An haifi Soba ne a 1949 sannan ya yi karatu a cikin gida da kasashen waje a fannoni da dama na mulki da ayyukan majalisar dokoki.

“Ya taba zama Akawun Majalisar Dokokin Jihar Kaduna.”