✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saki a fim: Yadda fatawar Dokta Bashir ta tayar da kura

Malamin ya yi cikakken bayanin hukuncin, amma masu ce-ce-ku-ce ba su daina ba

Masu tsokaci na ci gaba da ce-ce-ku-ce game da fatawar da Limamin Masallacin Al-Furqan da ke Kano ya yi game da sakin aure a cikin fim.

Kurar ta fara tashi ne bayan fitar wani bidiyo da aka yanko daga tafsirin Dokta Bashir Aliyu, inda yake cewa ba a sakin aure da wasa, sannan ya yi bayani cewa duk wanda ya yi sakin aure a fim da wasa, to matarsa ta gida ta saku.

Cikin dan lokaci bidiyo da aka tsakuro ya karade shafukan sada zumunta tare da jawo maganganu.

Bayan ce-ce-kucen da ya biyo bayan yaduwar bidiyon ne Dokta Bashir da ya fito a wani bidiyo inda ya ce ba fahimci bayaninsa ba, sanan ya yi cikakken bayanin hukuncin da ya yi magana a kai.

Wasu kuma na cewa yanke maganar da malamin ya yi a wurin karatunsa aka yi, aka fitar da bidiyon farkon da ya jawo rudani da surutai.

Misali, Yasir Ibrahim Gwale cewa ya yi, “Sun yanko wani sashi na bayanin da Malaminmu Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar Hafizahullah ya yi a cikin karatun Tafseer da ya yi mako uku da ya wuce, a kan sakin aure cikin shirin fim. [To] Malam ya yi bayani a kai,” sannan ya sako bidiyo da malamin ya yi cikakken karin bayani game da abin da yake nufi.

Duk da haka, mutane ba su fasa yin tsokaci a kan jawabin malamin ba.

Ibrahim Sanyi-Sanyi ya rubuta cewa, “Yauwa! malam ya yi wa fatawarsa kwaskwarima a bidiyo na biyu.

“Saki zai tabbata idan miji da mata suka fito a cikin fim, mijin ya furta ya saki matarsa a cikin fim ko da kuwa a cikin wasa ne.

“Da tun farko wannan ce fatawar malam, da ba a tsaya ana jayayya ba.”

Dokta Ibrahim Musa kuma cewa ya yi, “Fatawar Malam ta baya ta zo da karin haske. Sakin Kannywood bai saku ba, amma duk da haka daraktoci su lura kada a rika wasa da saki.

“Wadanda sukai shirin tamore suna jira darakta ya daura musu aure a fim, to ku sani kwalelenku. Ta leko, ta koma- an yi wa mai zani daya sata. Allah Ya kara wa Malam imani da ilmi.”

Ita kuwa fitacciyar ma’abociyar Facebook a Kaduna, Fatima Kaita cewa ta yi, “Duk iya tsiyar da za mu yi a wagga kafa ba za mu raina malamai ba. Allah Ya kara wa rayuwar malam albarka.”

Adamu Abdulkadir Kaura cewa ya yi, “Malamai su yi fatawa, jahilai su yi raddi, sai yaushe za a ba wa ilimi daraja?”

Abdulkadir Dan Nafisatu cewa ya yi “Idan dan wasan kwaikwayon da ya furta ‘na saki matata’ yana da mata fiye da daya, wacce ya saka?”

Nan sai Jafar Jafar ya amsa cikin barkwanci da cewa, “amarya mana.”

Shi ma Jafar Jafar ya wallafa a shafinsa cewa, “Maganar gaskiya Mallam fa ya yi kunu.”

Shi kuwa Aliyu Dahiru Aliyu cewa ya yi, “Ashe shi dakta ya dogara da wani ra’ifin hadisi ne wajen sakarwa su Ali Nuhu mata.

“Hadisin da har Albany ya ce ra’ifi ne shi ne aka yi amfani da shi wajen sakar wa su Adam A. Zango matansu.

“To Zango da kansa ma sakinsu yake balle kuma an sakar masa su.

“Kuma ina zaton dakta ya manta a wannan ra’ifin hadisin an lissafa cewa aure ma ba a wasa da shi. To ke nan duk auren da aka daura a fim ya dauru?”

“Ina tunanin su dakta ba su gane me ake nufi da wasa ba a nan ko da hadisin ya inganta.

“Ba maganar wasan Hausa ake ba. Magana ce ta ka je gun matarka ka ce ka sake ta sannan ka dawo ka ce da wasa kake, ba wai Ali Nuhu ya saki Rahma Sadau ba.”

Muhammad Shamsuddeen Muhammad kuma ya ce, “A kokarin yi mana karin bayani, kawai shi ma sai ya ce ya saki matarsa.”

Cikakken Fashin bakin Dokta Bashir

Daga bisani Dokta Bashir ya sake fitar da wani hoton bidiyo inda ya yi karin haske dangane da fatawar da ya yi kuma ya yi mata lakabi da “cikakken bayani a kan hukuncin wanda ya saki matarsa da wasa.”

Ya ce, “Zan yi bayani ne zuwa ga jama’ar Musulmi a kan bin da ya yadu a kafafiofin sada zumunta dangane da sha’anin saki da kuma abin da ya danganci ambatonsa a cikin wasan kwaikwayo.

“Wannan magana ta zo a cikin darasi na tafsirin Al-Kur’ani da muke yi a masallacin Al-Furqan wanda ya zamto ta sanya rudani a cikin fahimtar mutane wanda ya wajaba na yi bayani saboda a saita fahimta kan abin da shi ne na ambata.

“Da farko dai wannan magana ta zo a kan gaba ta bayanin tafsirin ayar Al-Kur’ani ta Suratul Taubah, wadda Allah Yake cewa mazonsa, ka ce musu ya Rasulullah, da Allah ne da ayoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna yi wa izgili?

“To a kan haka ne na yi bayanin cewa izgili da wargi da wasa idan ya danganci janibin Allah da Al-Kur’ani da Manzon Allah (SAW) yana da hadari, domin zai fitar da mutum daga addini.

“Sannan na ce izgili a kan abin da ya danganci hukunce-hukunce na Shari’a, to shi ma akwai wani babi wanda yake da hadari, shi ne abin da ya danganci saki, da aure da komen aure, saboda Manzon Allah (SAW) yana cewa, “abu uku gaskensu gaske ne, kuma warginsu ma gaske ne – saki da aure da kome.”

“To a kan haka ne, na ce idan mutum ya ce matansa na aure a cikin wasan kwaikwayo, wannan saki idan yana da matan a gaske, to wannan saki ya afku a kansu, sai dai maganar a dunkule take haka amma tana da tafsili (fashin baki).

“Idan mutum a cikin wasan kwaikwayo ya kalli matarsa ta wasan kwaikwayo, ya ce, ke kin saku, ko ke wance na sake ki.

“To za a duba a gani, idan wannan matar wadda take cikin wasan kwaikwayon matarsa ce ta hakika tun kafin su yi wasan kwaikwayo ya zamanto da ita da shi duk suna shiri ne a cikin wasan kwaikwayon;

“To idan ya kalle ta ya ce ya sake ta, duk da yake wasa ne, to wannan saki ya afku saboda wannan nassi na Hadisin Annabi (SAW).

“Amma idan wannan mata wadda take cikin wasan kwaikwayo ba matarsa ce ta aure ba, fim ne ko wasan kwaikwayo ne ya mayar da ita matarsa, to wannan saki bai samu mahalli ba, saboda haka matarsa ta aure babu abin da ya samu aurensa da ita.”

“Idan kuma ya zo yana bayar da labari ne a cikin shirin fim din, misali aka ce yana bayar da labari a wata fitowa a cikin shirin wanda ya zamto yana ba wa abokansa labari cewa, ‘to ai ni matana ma ga baki daya sun saku’, ko ya ce, ‘ai ni matata ma na sake ta’;

“To wannan maganar da ya yi, matarsa ta aure duk da yake ba ita yake nufi ba, idan har yana da matar ta aure, to wannan saki ya afku a kanta, saboda wannan Hadisi na Manzon Allah kuma saboda ayar Al-Kur’ani wadda Allah Yake cewa, ‘kada ku dauki ayoyin Allah su zama abin wasa’ kuma wannan ayar ta sauka ne a kan saki.

“Saboda haka wannan ita ce maganar da na fada a dunkule, amma wannan shi ne tafsilinta, kuma wannan magana ta cewa wanda ya fada da wasa, abu ne wanda haka yake a Mazhabar Malikiyya,

“Kuma haka yake Mazhabar mafiya yawan malamai, musamman Imamu Ahmad, wanda ya ce shi lafazin saki idan aka yi shi, ba a bukatar niyya, yana afkuwa ko mutum ya yi niyyarsa ko mutum bai yi niyyarsa ba.”

‘Amma kuma…’

“To sai dai akwai malamai a Mazhabar Malik da suke cewa idan akwai wata karina (alama ko shaida) da take nuna wasa yake yi, to wannan shaidar za ta taimaka masa ta nuna kan cewa sakin bai afku a kansa ba.

“Bisa wannan, wadanda suka riga suka yi irin wannan fitowa a cikin wasan kwaikwayo, alal misali wani daga cikinsu yana da aure a ciki, yake bayani a cikin wasan kwaikwayo, cewa ‘to ni na saki matata,’ to wannan tun da akwai shaidar kamar yadda aka ruwaito daga Ibn Al-Kasim duk da yake ba shi ne mashhurin mazhabar da ake fatawa a kai ba, to wannan ba zai bata aurensa ba, yana nan tare da matarsa.

“Makasudin wannan shi ne a nuna wa ’yan uwa wadanda suke cikin wannan sana’a ta harkar fim, kan cewa akwai (no go areas) abubuwa da ba za su yi ba, saboda tarbiyarsu ta addini:

“Abin da ya danganci sifar Allah babu wasa da wannan; abun da ya danganci Al-Kur’ani, babu wasa da wannan, abun da ya danganci Manzon Allah (SAW), babu wasa, babu izgili da wannan; abun da ya danganci aure da saki da kome, yin lafazi da su, babu wasu da wannan.

“To kowace al’umma tana da wuraren da aka yi mata shamaki, to ai ka ga duk wanda suke sha’anin harkar fim, sun san akwai wuraren da suke da iyaka.

“To mu ma saboda tarbiyarmu ta addinin Musulunci, ’yan uwa da suke cikin harkar fim, ya kamata su san irin wadannan iyaka da suke da ita.

“Akwai wurare da ba a tsallake su, ba a ketare su, an yi musu shamaki kada su ketara su je irin wannan wurare, wannan ita ce tarbiya ta addinin Musulunci.

“Kuma wannan maganar kamar yadda kuka gani, na gina ta ne a kan ayar Al-Kur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW) da kuma abin da shi ne mashhurin mazhabar Malik wanda a kansa fatawa take.”

Dokta Bashir a bidiyon na tsawon minti bakwai, ya tuke da cewa, “Allah Madaukakin Sarki Shi ne Mafi Sani.”