Sakon Bagizagen Mako | Aminiya

Sakon Bagizagen Mako

Bakonmu na wannan mako, shi ne tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya na Riko Malam Yunusa Abdullahi (08036066547), wanda a sakonsa yake cewa:

Assalamu alaikum, Gizagawan Zumunci. Zan fara jinjina wa Madugun Zumunci, Malam Bashir Yahuza Malumfashi da kuma jajirtaccen Shugabanmu Malam M. K. Adam Gombe, tare da haziƙan ’yan majalisarsa da suka dage wajen farfaɗo da harkokin Gizago; musamman a wannan kafa ta jaridarmu Aminiya mai farin jini. Allah (SWT) Ya ƙara muku himma, kwazo da basirar ɗaukaka wannan ƙungiya zuwa gaba.

Bayan haka, ina tunatar da mu cewa babbar manufar kafa wannan ƙungiya ita ce ZUMUNCI, saboda haka kowanemu ya tashi tsaye, ya dage wajen ba da tasa gudunmawar domin jaddada zumunci ta hanyar halartar tarurruka a matakin da muke da biyan kuɗin ƙa’ida da kuma uwa-uba, muna tuntuɓar junanmu ta kiran waya a-kai-a-kai.

Daga ƙarshe ina kira mu ƙara jajircewa wajen yi wa shugabanninmu biyayya tun daga matakin jiha zuwa ga kasa baki daya.