✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon Shekau: Sojoji da Fadar Shugaban Kasa sun yi gum

Mun nemi jin ta bakin rundunar tsaro da Fadar Shugaban Kasa amma abin ya gagara

Sama da kwana guda bayan kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin garkuwa da daliban Makarantar Kankara, Fadar Shugaban Kasa da Rundunar Tsaron Najeriya sun ki cewa uffan.

Bayan sakon sautin ranar Talatar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, cewa kungiyar ce ta sace daliban, mun yi kokarin jin ta bakin Fadar Shugaban Kasa da Rundunar Sojin Najeriya amma sun yi gum.

Babban Mashawarcin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Garba Shehu bai amsa kiran waya da rubutaccen sakon da muka tura masa ba har muka kammala hada wannan rahoton.

Ita ma Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta yi gum da bakinta game da ikirarin da Shugaban Boko Haram ya yi.

Mun yi ta kiran Babban Jami’in Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar John Enenche domin mu ji ta bakinsa amma bai dauka ba, bai kuma amsa sakon da muka aika masa ta waya ba.

Ita ma Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, ba ta amsa bukatarmu ta samun bayani game inda aka kwana kan batun ba.

Mai magana da yawun Rundunar, Birgediya Sagir Musa bai amsa kiran wayar da muka yi maasa ba.

 

‘Masari ya yi shiririta’

Wani tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Mike Ejiofor, ya shaida mana cewa bayanin da Gwamna Aminu Masari ya yi cewa gwamnati na tattaunawa da masu garkuwar ba ta da amfani.

Ejiofor ya ce: “Ban ga dalilin da gwamnati za ta fito ta cewa tana tattaunawa da ’yan bindigar ba”.

Tsohon shugaban na DSS ya ce babu bambanci tsakanin Boko Haram da ’yan bindiga tunda kowannensu manyan laifuka yake aikatawa.

“Ikirarin na nufin da karfinsu kuma sun bazu a sassan kasar na. Tunda har suka iya zuwa Arewa ta Yamma suka yi garkuwa da adadin mutanen da ba su iya yi ba a Arewa  maso Gabsa, to muna bukatar mu tashi wurjanjan”, inji Ejiofor.

 

A daina biyan kudin fansa

A nasa bangaren, mai sharhi kan ayyukan ta’addanci da kuma tara bayanan sirri na kasa da kasa, Dokta Amaechi Nwaokolo, ya yi kira da a daina biyan ’yan ta’adda kudaden fansa.

A cewarsa hakan na nufin tamkar gwamnatin kasar na tallafa wa ’yan ta’adda da kudade ne.

“’Yan bindigar na da alaka da Boko Haram. An gano cewa ’yan ta’adda na hada kai su yi aiki da gungun masu aika manyan laifuka; saboda haka tamkar ana ba wa masu laifi kudade ne” kamar yadda ya bayyana.

 

Babu gaskiya a bayanan masari

Wani Masani a kan harkar tsaro, Malam Kabir Adamu Matazu, ya ce babu kamshin gaskiya a maganar da Gwamna Masari ya yi cewa sun fara tuttaunawa da ’yan bindigar da suka sace daliban.

Idan ba a manta ba Masari ya shaida wa Shugaba Buhari cewa ’yan bindigar da suka dauke yaran sun tuntube su kuma an fara tattaunawa da su don su sako daliban.

Sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar bayan gawanar gwamnan ta Buhari ta ambato Masari na cewa an gano inda aka kai yaran kuma sojoji sun yi wa wurin kawanya.

“Abun takaici, sai ga Shekau ya fito ya fita yana cewa su ne suka dauke daliban.

“Wannan ya nuna yadda gwamnati ke rufa-rufa da abubuwa, sun yi waccan maganar ce domin su kwantar wa iyayen daliban hankali”, inji masanin”, inji shi.