Daily Trust Aminiya - Sakonni zuwa ga FDK
Subscribe

Sakonni zuwa ga FDK

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Yau ma kamar kullum, ni FDK ban yi nukusani ba, zaune nake a karagata, a lokacin da na fara bude sakonninku, na fara karantowa cikin nishadi da annashuwa, kamar haka:

Daga Ibrahim Musa Fagge (08069412310):

FDK, ina maka fatar alheri tare da fatar kana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka. Gaskiya ina jin dadin irin maudu’o’in da kake gabatar mana. Allah Ya kara daukaka, amin.

Daga Abdul Funtuwa (09017872733):

FDK, da fatar kana cikin koshin lafiya da kai da duk wanda yake bibiyar wannan shafi na Dausayin Kauna. Bayan haka, jama’a kada mu shagaltu, mu kasance masu bibiyar wannan shafi mai hada zumunci domin jin yadda Labarin Farida zai kasance. FDK, ina rokonka ka mika min sakon gaisuwa ga Nafisat Dutsin-ma. A karshe ina muku fatar alheri, na gode.

Daga Sabi’u Nura Maiduguri (08133388888):

Aminicin Allah ya tabbata ga ma’abuta wannan fili na Dausayin Kauna mai albarka da kuma uban gayya FDK. Gaskiya muna matuƙar ƙaruwa da Labarin Farida, Allah Ya ba ka ikon ƙarasa mana shi.

Daga Yunus M. Saleh (08056333326):

FDK, wai me ya sa wadansu mazan ke boye wa matansu muhimman al’amura ne? Banga dalilin da Mamman zai ba Baba wannan shawarar ba.

Daga Musa Maidoki Gawuna (09022205720):

Barka da fama da jama’a FDK, da fatar alheri ga dukkan ma’abota bin shafin nan na Dausayin Kauna. Ina son a isar min gaisuwata a gare su. Allah Ya kara maka karfin gwiwa da lafiya, domin mu ji karshen Labarin Farida.

Umar Kano Sarkin Yakin FDK (07035438533):

FDK, ina gaida dukkan masoya masu ninkaya cikin kogin Dausayin Kauna. Har yanzu muna jiran fitowar littafin Labarin Farida, wanda ka ce zai fito tun bara.

Daga Sulaiman Senior Mowe Jihar Ogun:

FDK, fatar alheri gare ka da kuma duk masu bibiyar wannan fili naka. Don Allah ina bukatar addu’ar jama’a, Allah Ya ba ni mace tagari, amin-summa-amin.

Daga Ahmed Baban Sadik (09034255366):

Ina matukar jin dadin shirye-shiryenku. Ina muku fatar alheri dukkanku, Allah Ya bar zumunci.

Daga Fadila Mpape Abuja (08126875130):

Allah Ya taimaki FDK da duk wanda ke bibiyar wannan shafin, amin. Ni bakuwa ce amma na dade ina bibiyar wannan shafi.

Daga Asiya Sakkwato:

Jinjina ga FDK da kuma masu bibiyar wannan shafi na Dausayin Kauna. A gaskiya wannan labari na Farida yana ba mu nishadi, Allah Ya kara basira, amin.

More Stories