Daily Trust Aminiya - Salah na dab da karya tarihin da Didier Drogba ya kafa

Mohammed Salah

Salah na dab da karya tarihin da Didier Drogba ya kafa

Dan wasan gaba na Masar da yake taka leda a Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool Mohamed Salah, yana dab da karya tarihin da Didier Drogba na Ivory Coast ya kafa a gasar Firimiya ta Ingila.

Drogba wanda ya taka leda a Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea shi ne dan wasan Afirka mafi zura kwallo a gasar Firimiya ta Ingila inda yake da yawan kwallaye 104 a zamanin taka ledarsa.

Yanzu haka Mohammed Salah na Masar yana da kwallaye 103 da ya zura a karkashin gasar ta Firimiya bayan ya ci kwallonsa a wasan da suka yi canjaras da Manchester City da ci 2 da 2 a karshen mako.

Dan wasan na Masar mai shekara 29 yana neman kwallo guda ce kacal ya kamo Drogba.

Masana wasanni suna ci gaba da kwatanta tauraron na Liverpool da manyan ’yan kwallo irin su Ronaldo da Messi musamman bayan ya ci kwallo a wasan na ranar Lahadin makon jiya wadda aka bayyana da mafi kayatarwa a kaf kwallayen Firimiya.

Mohamed Salah na ci gaba da nuna bajinta a wasannin Liverpool bayan sayo shi daga Roma a shekarar 2017 inda yake matsayin dan wasa mafi zura kwallo a kusan kowace kaka.

Shi ma mai horar da Kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana kwallon ta Salah a matsayin wadda za a shafe shekara 60 duniyar kwallo ba ta manta da ita ba.

Karin Labarai