✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Salah ya kafa sabon tarihi a Liverpool

Liverpool ta kafa tarihi a kan Manchester United a filin wasa na Anfield.

Dan wasan gaban Liverpool, Mohamed Salah, ya kafa sabon tarihi zama wanda ya fi zura kwallaye a Gasar Firimiyar Ingila.

Mohammed Salah dan kasar Masar ya ci wa Liverpool kwallonsa ta 129 a karawar da suka yi da Manchester United a ranar Lahadi.

Da hakan, Salah ya sha gaban Robbie Fowler, wanda ya ci kwallaye 128 a gasar a zaman da ya yi sau biyu a filin wasa na Anfield, sai Steven Gerrard mai kwallaye 120 a matsayin na uku.

Michael Owen, ya ci gaba da zama a matsayi na hudu a jerin, bayan da ya zura kwallaye 118 a gasar, yayin da Sadio Mane ya ci 90 ke a matsayi na biyar.

Wannan gagarumar nasarar ta Salah ta zo ne yayin da ya zura wa Liverpool kwallaye biyu da suka yi nasara mai ban mamaki da ci 7-0 a kan abokanan hamayyarsu Manchester United a filin wasa na Anfield, inda ya buga wasa na 205.

Dan wasan da ke sanya lamba 11 ya fara zura kwallo ne a gasar Firimiyar Ingila a wasan Liverpool ta buga a Watford a watan Agustan 2017 bayan ya kammala komawa kungiyar daga AS Roma a farkon kakar wasanni.

Yayin da ya fara buga wa kungiyar a kakar wasannin ta 2017-2018 ya zura jimlar kwallaye 32, inda ya lashe kyautar takalmin zinare na farko a lokuta daba-daban har sau uku zuwa yanzu, wanda ya hada da kakar wasanni ta 2018-2019 da kuma 2021-2022.