✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah Karama: Abubuwan da ya kamata a aika

Abubuwan da malamai suka kwadaitar a aikata da Karamar Sallah.

Ranar Sallah rana ce ta farin ciki da nuna godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan lafiya.

Abubuwan da malamai suka kwadaitar a aikata da Karamar Sallah su ne:

  1. Yin kabbarori da zarar an ga watan Shawwal.
  2. Wankan idi kafin zuwa masallacin idi a ranar Sallah.
  3. Sanya sabbin kaya ko mafiya kyawunsu don zuwa idi.
  4. Yin ado da fesa turare (ga maza).
  5. Cin abinci kafin tafiya masallacin idi.
  6. Tafiya sallar idi a kan lokaci.
  7. Zuwa tare da mata da kananan yara.
  8. Yin kabbarori a bayyane yayin tafiya idi.
  9. Ba a yi wa sallar idi kiran sallah.
  10. Babu nafila kafin sallar idi ko bayanta.
  11. Yin sallar idi a bayan liman.
  12. Sauraron hudubar bayan sallar idi.
  13. Taya juna murna da fatan alheri.
  14. Sauya hanyar dawowa daga idi.
  15. Sadar da zumunci a lokacin idi.
  16. Bayar da kyaututtuka.