✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: Ranar Talata za a fara neman wata —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya ce a fara neman watan Karamar Sallar bana daga ranar Talata.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci Musulmin Najeriya da su fara duban jinjirin watan Karamar Sallah na Shawwal daga ranar Talata.

Sarkin Musulmi ya ranar Talata da za a yi duban farko, ita ce 29 ga watan Ramadan, 1442 Hijiriyya, kamar yadda Mataimakin Sakataren Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) Farfesa Salisu Shehu ya sanar a ranar Asabar.

Ya ce, “A shirye-shiryen Karamar Sallar 1442 Hijiriyya, Kwamitin Ganin Wata na Kasa (NMSC), karkashin NSCIA ya shawarci Sarkin Musulmi cewa a fara duban wata Shawwal daga ranar Talata, 11th ga Mayu, 2021 wato 29 ga Ramadan, 1442 Hijiriyya.”

Don haka ya bukaci daukacin al’ummar Musulmin Najeriya da su fara neman sabon watan a ranar, bisa umarnin Sarkin Musulmi, domin kammala azumin watan Ramadan na bana.

Ya kuma bayyan lambobin tuntubar Kwamitin Ganin Wata na Kasa ga duk wanda Allah Ya sa ya ga watan na Shawwal.

“Idan an ga watan, masana za su ba Sarkin Musulmi shawarar abin da ya dace sannan ya yi taron ’yan jarida ya sanar da cewa Laraba, 13 ga Mayu 2021 ita ce ranar Karamar Sallah.

“Idan kuma ba a ga watan a ranar Talatar ba, to kai tsaye Alhamis, 13 ga Mayu, 2021 ita ce ranar 1 ga Shawwal, 1442 Hijiriyya (wato ranar Karamar Sallah). Za kuma a sanar da hakan a ranar Talata,” inji Farfesa Salisu Shehu.