✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai gidan jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah ya rasu

Allah Ya yi wa Mista Sam Nda-Isaiah mai jaridar Leadership ta Najeriya rasuwa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Mista Nda-Isaiah ya rasu ne a…

Allah Ya yi wa Mista Sam Nda-Isaiah mai jaridar Leadership ta Najeriya rasuwa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Mista Nda-Isaiah ya rasu ne a Abuja a daren Asabar yana da shekara 58.

Wani makusancinsa ya ce mamacin ya rasu ne bayan “Bayan an kai shi asibitin Nizamiye da ke Abuja inda likitoci suka kula da su.

“Da rashin lafiyar ta yi tsanani sai aka mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada inda Allah Ya yi masa rasuwa a cikin daren Asabar”.

Tuni dai shugabanni da fitattun ‘yan Najeriya daga bangarorin rayuwa da dama ke bayyana jimaminsu game da rasuwarsa, suna masu yabawa da kyawawan halayensu.

A ranar Talata, Mista Nda-Isaiah wanda tsohon mai zawarcin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ne ya halarci taron shekarar 2020 na Kungiyar Masu Gidajen Jarida na Najeriya (NPAN) a Legas inda aka zabi sabbin shugabanni.

Bayan halartar taron NPAN cikin koshin lafiya inda ya aka zabe shi cikin jagororin kungiyar, Mista Nda-Isaiah ya kasance cikin koshin lafiya har zuwa ranar Laraba, bayan komawarsa Abuja, inda ya gana da jama’a.