✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samamen DSS a ofishin NNPP ya bar baya da kura

Shugaban NNPP ya zargi hukumar DSS da yi wa ’ya’yan jam'iyyarsa kazafi.

NNPP a Jihar Kano ta zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kokarin muzguna wa ’ya’yanta baya hukumar ta kai samame ofishin yakin zaben jam’iyyar.

Sai dai cikin wani martani da hukumar ta fitar, ta ce ta kai samamen ne domin kwace wasu makamai a ofishin jam’iyyar, kuma haka ta yi wa kowace jam’iyya da ke takara a jihar.

Zargin na NNPP na zuwa ne bayan wanda ta yi wa tsohon kwamishinan ’yan sandan jihar, Mamman Daura, da hada baki da gwamnatin jihar wajen kame ’ya’yan jam’iyyar.

Kwanaki kadan bayan zargin na farko, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan  Najeriya, Usman Baba Alkali ya sauya wa kwamishinan wurin aiki zuwa Jihar Filato.

An aike sabbin Kwamishinan ‘yan sanda uku da mataimaka zuwa jihar don tabbatar da an gudanar zaben ranar Asabar cikin lumana.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban jam’iyyar NNPP a jihar, Umar Haruna Doguwa, ya ce DSS ta kai wa ofishin daraktocinta samame.

“Mun kadu da yadda jami’an DSS suka dinga debo makamai daga motocinsu suna jibgewa a ofishin daraktocinmu a kan idon ma’aikacin yakin neman zabenmu, kuma ya nadi bidiyon yadda lamarin ya gudana. Muna da hotuna da bidiyo na abin da ya faru.

“Muna kira ga Darakta-Janar na DSS da ya kafa oda a Kano,” in ji Doguwa, kana ya ce yana da kyau DSS ta guji kokarin “Yi wa ’ya’yan jam’iyyarsa kazafi.”

Kazalika, shugaban jam’iyyar ya zargi Daraktan DSS da hade kai da gwamnatin jihar, inda ya ce tun shekarar da ta wuce lokacin ritayarsa ya yi amma an ki sauya shi, saboda bukatar kai ta gwamnatin jihar.

Ko da Aminiya ta tuntubi kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyan cewa jami’ansu sun kwato muggan makamai kamar bindigogi, takubba, adduna, wukake da sauransu daga wasu ’yan siyasa.

Afunanya ya aike wa Aminiya wasu hotuna na muggan makaman da suka kwato ta WhatsApp, inda ya ce, “Shin wadannan su ne kayan yakin neman zabe?”

Ya ce, “An binciki ofishin ne da izinin kotu. Abin da suke fada game da abin da ya faru ba gaskiya ba ne. DSS a Kano ba ta yi wa kowace jam’iyya barazana ba a jihar.”

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu samu jin ta bakin Kwamishinan ’Yada Labaran Gwamnatin Jihar, Muhammad Garba don jin ta bakinsa kan lamarin.