✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samar da makamai ga jama’a don kare kai: A jaraba tsarin Zamfara

Me zai hana a jarraba tsarin na Zamfara?

Ina fata lokacin da mai karatu yake karanta wannan makala, shirin nan na tantance mutanen Jihar Zamfara da ke da shaawar su mallaki makamai a lungu da sakon jihar, don kare kansu daga hareharen ’yan bindiga ya kankama a dukkan masarautun jihar 19.

Jihar Zamfara na cikin jihohin Arewa, irinsu Katsina da Sakkwato da Kaduna da Neja da Taraba da Filato da sauransu da suke fama da annobar hare-haren ’yan bindiga masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, wani lokaci ma in ajali ya gitta koda an biya kudin fansar, su kuma kashe wanda sukai garkuwar da shi.

A cikin laluben yadda za su kawo karshen wannan annoba da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa, ya sanya wasu daga cikin wadannan jihohi suka jaraba yin sulhi iri-iri da ’yan bindigar, sulhun da ya hada da tattaunawa da sake tsugunnar da ’yan bindigar da shirin mika makaman wadanda suka tuba ga mahukunta.

Har wasu kasuwanni jihohin suka jaraba rufewa, yayin da wasu suka sa aka katse hanyoyin sadarwa duk dai a zaman yadda shawo kan al`amarin. Baya ga tattaunawar da gwamnonin sukan yi ya junansu da Gwamnatin Tarayya ko da kasashen makwabta irin su Jamhuriyar Nijar.

Asarar rayuka da ta dukiya da wadanda aka jikkata ko aka mayar da su ’yan gudun hijira a cikin kasarsu kuwa sai dai a kiyasta.

Kusan kullum garin Allah Ya waye sai ka ji labarin harin ’yan bindigar da barnar da suka yi. Koda a wancan makon ’yan bindigar da ake zargin su suka kai wa ayarin Shugaban kasa hari a hanyar Dutsin-ma a cikin Jihar Katsina, su ake zargi da yin kwanton bauna tare da kashe Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Aminu Umar, lokacin da suka je wani aikin kakkabe sua dajin Zakkah na karamar Hukumar Safana.

Haka kuma ana zargin ’yan bindigar da suka tsare jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a cikin watan Maris da ya gabatar, su dai ne a cikin wannan watan suka kai wani mummunan hari a gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda suka saki mazauna gidan da dama ciki kuwa har da ’yan kungiyarsu.

Ba sai an fada ba, gajiya da irin annobar ’yan bindigar ta sanya a ranar Lahadi 26 ga watan Yunin da ya gabata Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya umurci Kwamishinan ’Yan Sandar jihar da ya ba da lasisin mallakar bindiga ga ’yan asalin jihar masu bukatar haka, don kare kansu daga hare-haren ’yan bindigar a karkashin wani shiri mai suna “Shirin Tsaron Al`umma.”

A karkashin shirin, za a tace mutum 500, daga kowace masarautar jihar, daga cikin masarautu 19 da ake da su, wanda zai ba da jimillar mutum 9,500. Sarakuna iyayen al`umma tun da daga ungunni, su aka dora wa alhakin tantance masu sha`awar mallakar makaman.

Bayan sun kammala ne za su mika wa gwamnatin jihar, wanda bayan ta gama tata tantancewar za ta mika wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar don amincewa ta karshe da ba da lasisi ga wadanda suka haye siradin da aka gitta.

Domin samun nasarar shirin gwamnatin jihar ta kafa wasu kwamitoci hudu da suka hada da Kwamitin Tattara Bayanan Sirri A Kan ’Yan Bindiga da Kwamitin da zai rinka gurfanar da ’yan bindigar da aka kama da laifin kai hare-hare da makamantan laifuffuka.

Sai Kwamitin da zai rika bin diddigin wadanda aka ba lasisin mallakar bindigar da kuma zaunannen kwamitin tsaro na jihar. Da yake kaddamar da kwamitocin a Gusau, Gwamna Matawalle ya ce ba gudu ba ja da baya a kan wannan aniya da gwamnatinsa ta sa gaba, yana mai jaddada cewa kare kai na daga cikin dabarun dan Adam a kan yadda zai rayuwa tun asali.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta gudanar da wannan sabon shiri da a bisa ga tanade-tanaden dokokin kasar nan.

Tun da Gwamna Matawalle ya furta aniyar wannan shiri, yake ta samun suka daga masana matakan tsaro da jami`an gwamnati. Alal misali, masana tsaro na fargabar cewa ’yan kasa su mallaki makamai don kare kai zai iya jefa kasar cikin hayaniya da rudani a kan harkar tsaro.

Shi kuwa Babban Hafsan tsaron kasar nan, Janar Lucky Irabor, cewa ya yi bai san dokar da ta ba gwamnan jiha ikon ya umurci Kwamishinan ’Yan Sandan Jiha a kan ya ba da lasisin mallakar bindiga ga mutanen jiharsa ba. A takaice Babban Hafsan yana nufin gwamnan jiha ba shi da ikon hakan.

A ra’ayina masu maganar ’yan kasa su mallaki lasisin bindiga zai jefa kasar nan cikin hayaniya da rudani, sun manta da cewa yanzu din ma kasar cikin yaki take ba ma hayaniya da rudani ba? Shi kuma Babban Hafsan Tsaro, ba wani abu yake ba illa nade tabarmar kunya, kasancewar dakarunsa sun gaza kawo karshen wannan rashin tsaro.

Ina ganin yanzu ya kamata duk wani tarnaki da aka sa na hana ’yan kasa su mallaki lasisin mallakar bindiga ya kamata a janye shi ga mutanen Jihar Zamfara, ta yadda za su jaraba wannan shiri.

Ana cewa akwai haramci, su ’yan bindiga da suka dauki makamai a kan sauran ’yan kasa wa ya ba su izini? Bare kuma mutunen da ake kwana ana tashi da su, wadanda za su yi aiki a kungiyance don ceton kansu da al`ummarsu? An dai ga irin rawar da ’yan kungiyar sa kai na Jihar Borno suke takawa a yaki da ’yan kungiyar Boko Haram.

Ina kuma da labari, a wasu jihohin da annobar ’yan bindiga ta yi kamari, akwai kauyukan da ’yan bindiga ba sa iya kai masu hari, kasancewar mutanen kauyukan kullum a shirye suke, ba sa barci dare da rana da makamansu na farauta suna tsaron kansu kuma sun samu saukin hare-haren ’yan bindigar.

Ina a ce za su mallaki makamai irin wadanda ’yan bindigar suka mallaka. Don haka Gwamnatin Tarayya ki bari a jaraba shirin Zamfara kawai.