✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon Shugaban APC na kasa

Dukkanin masu neman kujerar sun janye wa Sanata Adamu.

An sanar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru  wanda shi ne shugaban karamin kwamitin babban taron ne sanar da hakan bayan duka wadanda suke takarar sun janye wa Abdullahi Adamu.

Kafin sanar da sabon shugaban, sai da Gwamna Badaru ya tambayi wakilan zabe ko kuma deliget kan cewa sun amince da Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban APC, sai suka ce sun amince.

Tun kafin a soma taron dama ana ta rade-radin cewa za a samu maslaha a ba Abdullahi Adamu shugabancin, inda a yayin taron ne masu takarar suka sanar da cewa duk sun janye.

A ranar Asabar ce Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa domin zaben sabon shugabanta tare da shawo kan rikicin cikin gidan da take fama da shi.

Wasu bayanai dai na cewa gabanin fara babban taron na APC, wasu mutane 6 da ke shugabancin jam’iyyar sun janye daga takarar, inda suka marawa abokin takararsu Sanata Abdullahi Adamu baya bayan cimma maslaha.

Rahotanni sun ce Sanata Adamu dai shi ne dan takarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke marawa baya.

Sa’o’i kadan kafin fara gudanar da babban taron jam’iyya mai mulkin Najeriyar ta APC, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda take kalubalantar tsarin mulkin APCn, tare da neman a bayyana taron na ta a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Jam’iyyar ta PDP, ta kuma bukaci kotun da ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, ta soke rajistar jam’iyyar APC.

Cikin karar da ta shigar, PDP ta yi ikirarin cewa dukkanin tsarin jam’iyyar APC ya sabawa kundin tsarin mulki na tafiyar da jam’iyyar siyasa.