✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya zama shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma

Sauran mukaman shiyyar an cimma matsaya ta hanyar maslaha.

Tsohon wakilin shiyyar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya zama zababben shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma, bayan samun kuri’u 426, inda ya doke takwaransa Mohammed Yusuf wanda ya samu kuri’u 313.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin da ta gabata ce taron jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma ya gudana a filin wasa na Sir Ahmadu Bello da ke Jihar Kaduna, wanda kuma rikici ya biyo bayansa.

A watan Afrilun bara ne bata-gari suka kai farmaki a harabar gudanar da zaben inda suka yi awon gaba da akwatunan zabe tare da lalata kayayyaki, wanda hakan y kai ga dakatar da taron.

Sai dai a lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben a daren ranar Litinin, shugaban Kwamitin Zaben na shiyyar Arewa maso Yamma, Sanata Attah Aidoko Alli, ya yaba wa wakilai da hukumomin tsaro bisa yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya ce duk sauran mukamai an samu damar cimma matsaya ba tare da hamayya ba.