✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Danbaba ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Sanatan ya kara da cewa manufofin jam'iyyar APC sun yi daidai da ra’ayinsa na kashin kansa.

Sanata Ibrahim Danbaba mai wakiltar Sakkwato ta Kudu ya sauya sheka daga babbar  jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa APC.

Danbaba ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya rubuta wadda shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zaman Majalisar na ranar Laraba.

Ya ce dalilinsa na barin jam’iyyar PDP shi ne irin rikice-rikicen da PDP ke fama da su a Jihar Sakkwato.

Sanatan ya kara da cewa manufofin jam’iyyar APC sun yi daidai da ra’ayinsa na kashin kansa.