✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Gobir ya zama sabon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa

Ya maye gurbin Sanata Yahaya Abdullahi da ya sauya sheka PDP

Shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya zabi Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar Sokoto ta Gabas a matsayin sabon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa.

Matakin na jam’iyyar na kunshe ne a cikin wata wasika da ta aike wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan, mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu.

Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a farkon zaman majalisar na ranar Laraba.

Gobir ya maye gurbin tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Yahaya Abdullahi, daga (Kebbi ta Arewa), wanda ya sauya sheka zuwa PDP.

Kafin nadin nasa, Sanata Gobir ya jagoranci Kwamitin Tsaro da Leken Asiri na Majalisar.

Wasikar ta ce, “Dangane da wasikarka mai lamba: NASS9thS/SP/D/12/ mai dauke da kwanan wata 16 ga watan Yunin 2022, inda ka sanar da majalisa zabin jam’iyyarmu a majalisar dattawa.

“Ka yarda da wannan nadin da jam’iyyar ta yi wa Sanata Ibrahim Gobir a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon Shugaban Masu Rinjaye a majalisar.

“Ina na gode muku kan yadda kuke ba mu hadin kai.”