✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Goje ne ya fi dacewa da Shugabancin APC — Kungiyoyin matasa

Gamayyar Kungiyoyin Matasa magoya bayan jam’iyyar APC guda 150 masu mambobi kimanin dubu 100 a yankin Arewa maso Gabas, sun yi kira ga Sanata Muhammad…

Gamayyar Kungiyoyin Matasa magoya bayan jam’iyyar APC guda 150 masu mambobi kimanin dubu 100 a yankin Arewa maso Gabas, sun yi kira ga Sanata Muhammad Danjuma Goje, tsohon Gwamnan Jihar Gombe da ya fito takarar shugabancin jam’iyyar na kasa.

Shugaban Kungiyar Ci gaban Arewa maso Gabas, Kwamred Ahmad Afauwala ya ce da amincewar shugabancin jam’iyyar ta APC a jihohin yankin, gamayyar ta ayyana mara wa Sanata Gojen baya.

Ya ce sun zaga daukacin jihohin yankin guda biyar inda a karshe suka hadu a Gombe domin nuna goyon bayan su tare da kiran Danjuma Goje da ya fito takarar shugabancin jam’iyyar.

A cewarsu, tsohon gwamnan tun yana minista ya kawo abubuwan raya kasa a fadin Najeriya, sannan ya yi gwamnan Jihar Gombe har sau biyu inda yanzu yake Sanata karo na uku.

Sun ce yana da duk kwarewar da ake bukata na rike shugabancin jam’iyyar.

“Ganin yadda ya iya hade kan ’ya’yan jam’iyyar APC a kasa baki daya kuma muke ganin babu  wani sama da shi hakan ya sa muke kiran sa da ya amince ya tsaya neman wannan kujera ta shugaban jam’iyyar a kasa,” inji shugaban kungiyar.

A jawabinsa, Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Nite Amangal wanda mataimakinsa, CSP Ado Gabanni ya wakilta ya jijinawa matasan kan wannan tunani da suka yi na zabo uban siyasar Gombe ya zama Shugaban jam’iyyar a matakin kasa.

Sannan ya tabbatar wa da kungiyar cewa jam’iyyar a matakin jiha tana tare da su kuma za su goya musu tare da dafa musu a yakin neman zaben.

Shi kuwa sakataren jam’iyyar a jihar, Abubakar Adamu August, ya ce yana da yakinin Sanata Goje zai amsa kiran matasan.

Taron ya gudana ne a Sakatariyar Jam’iyyar ta APC da ke Gombe inda wakilai daga yankunan jihohin Arewa maso Gabas suka samu halarta.