✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Lawal da Gwamna Buni sun bude sabuwar Kasuwar Gashua

Mutanen Gashua za su kasance masu godiya a gare ku.

An yi bikin kaddamar da sabuwar kasuwar zamani ta Gashua Ultra Modern Market mai dauke da shaguna 505 a garin Gashuwa da ke Jihar Yobe.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da Gwamna Mai Mala Buni ne suka jagoranci bude sabuwar kasuwar a ranar Asabar.

A jawabinsa na maraba, Shugaban Karamar Hukumar Bade, Sanda Kara Bade, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun yaba da aikin.

Ya mika godiyarsa ga Gwamna Buni bisa aiwatar da ayyuka daban-daban da suka shafi jama’a a yankin.

A nasa jawabin na fatan alheri, Mai Martaba Sarkin Bade kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Yobe, Alhaji Abubakar Sulayman, ya yaba wa gwamnan kan gina sabuwar kasuwar.

“Mutanen Gashua za su kasance masu godiya a gare ku,” in ji Sarkin.

A nasa bangaren, Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci na Yobe, Alhaji Barma Shettima, ya bayyana sabuwar kasuwar a matsayin aiki mai inganci da ya dace da tsarin duniya wanda zai samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci.

Wani sashe na shaguna a sabuwar kasuwar

Shi ma Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Bade, Alhaji Babangida Sabo, a madadin mambobinsa ya gode wa gwamna Buni kan wannan aiki da ya ce zai taimaka matuka wajen bunkasa harkokin tattalin arziki.

Da yake mayar da martani, Gwamna Buni ya ce, an yi wa kasuwar rajista a matsayin kamfani mai iyaka, kuma an kafa hukumar da za ta tafiyar da harkokin kasuwar.

Wani sashe na sabuwar kasuwar Gashuwa

Ya bayyana cewa, kasuwar za ta zaburar da harkokin tattalin arziki ga al’ummar yankin yayin da yake kira ga mahukuntan kasuwar da su jajirce wajen mika kudaden shiga ga gwamnati yadda ya kamata.

Gwamna Buni ya sanya wa kasuwar sunan Shugaban Majalisar Dattawan la’akari da kasancewar dan kasa kuma Shugaban Majalisar Dattawa na farko da ya fito daga jihar da ma yankin na Arewa maso Gabas baki daya.

Da yake nasa jawabin, Sanata Lawan ya ce saboda kokarin gwamnan, kungiyar SAIL Foundation tana bayar da gudunmawar Naira miliyan 200 ga kananan ‘yan kasuwa 400 da masu kananan sana’o’i da manoma domin bunkasa tattalin arziki a yankin.

Shaguna a sabuwar kasuwar Gashuwa