✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata Shehu Sani ya sauya sheka zuwa PDP

Ya fice daga jam'iyyar PRP bayan wata ganawa da kushon jam'iyyar PDP.

Tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya sauya sheka daga jam’iyyar PRP zuwa jam’iyyar PDP.

Da yake tabbatar da sauya shekar, kakakin tsohon dan majalisar, Suleiman Ahmed ya ce uban gidan nasa ya tabbatar da sauya shekar tasa ce bayan ganawarsa da kusoshin jam’iyyar PDP a Kaduna ranar Alhamis.

Suleiman Ahmed ya ce, “Haka ne Sanata Shehu Sani ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP, amma za a yi hakan a hukumance ne nan da mako biyu masu zuwa”.

Shehu Sani ya kasance dan Majalisar Dattawa a karkashin inuwar jam’iyyar APC daga 2015 zuwa 2019.

Gabanin babban zaben shekarar 2019 ne dan majalsiar ya fice daga APC zuwa PRP, bayan wata takaddama a kan tikitin neman takararsa ta komawa kan kujerarsa, tsakaninsa da bangaren Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Bayan ya gaza samun tikitin takarar a APC ne ya fice ya koma PRP, inda ya samu tikiti, ya kuma kara da Sanata mai ci a yanzu, Uba Sanata, wanda ya kayar da shi a zaben.

Bayan ficewarsa daga PRP a yanzu, Shehu Sani bai bayyana ko yana da muradin sake fitowa takara ba a zaben 2023, amma ya ce yana tuntubar makusanta kan matakin da zai dauka na gaba.

A halin yanzu dai babu wani tabbaci game da irin matsayin da zai iya nema a 2023, amma ana hasashen zai iya namen sake komawa kan kujerarsa ta sanata ko kuma ya nema a bangaren zartarwa.