✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata ya yi wa daliget alkawarin kujerun aikin Hajji bayan sun kayar da shi

Sanata Smart Adeyemi ya yafe wa daliget kudaden da ya ba su, ya kuma yi musu alkawarin kujerun aikin Hajji

Sanata Smart Adeyemi ya yi alkawarin bayar da kujerun aikin Hajji ga daliget din da suka ki jefa mishi kuri’a a zaben dan takarar Sanata na mazabarsa da ya fadi.

Sanata Smart Adeyemi, wanda ke wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya yi alkawari ne bayan  wasu daliget sun yi tattaki har zuwa Abuja suka mayar mishi da kudaden da ya ba su gabanin zaben fitar da dan takarar.

Ya ce daliget biyar daga Karamar Hukumar Koton Karfe sun mayar da kudaden da ya ba su na “hawa mota da masauki da kuma cin abinci” bayan sun ki su jefa mishi kuri’a a zaben tsayar da dan takara.

Ya bayyana cewa rikon amanar daliget din ya burge shi, don haka ya bar musu kudaden sannan ya yi wa kowannensu alkawarin kujerar Hajji a shekarar 2023.

Alkawarin dan Majalisar Dattawan ta zo ne bayan ya ci kasa a yunkurinsa na yin tazarce a kujerarsa ta Sanata mai wakiltar Mazabar Kogi ta Yamma.

Yadda Sanata Smart Adeyemi ya fadi zaben dan takara

Adeyemi dai ya zo na uku ne a zaben fitar da dan takara da jam’iyyar APC ta gudanar a mazabar a ranar 28 ga watan Mayu, 2022.

Sakamakon zaben ya nuna Sunday Karimi ne lashe da kuri’a 288, sai Muyiwa Aina da kuri’a 73 a matsayi na biyu, sannan Sanata Smart Adeyemi a matsayi na uku da kuri’a 43.

Daliget din jam’iyyu dai sun samu miliyoyin Naira daga hannun masu neman tikitin takara da ke neman kuri’unsu.

‘Shiririta aka yi ba zabe ba’

Da yake jawabi kan sakamakon zaben da ya fadi, Sanata Smart Adeyemi, ya bayyana abin da ya faru a matsayin tozarci ga tsarin dimokuradiyya da kuma fashi rana tsaka rana ta hanyar murde zabe.

Ya bayyana cewa ya tsaya neman sake takarar ne be da son ran Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kogi, Abdullahi Bello ba.

Ya zargi shugaban jam’iyyar da neman ya janye ya mara wa gwamnan jihar, Yahaya Bello baya a kokarinsa na zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sai dai ya ce an tashi baram-baram a wani zama da shugaban jam’iyyar ya kira, bisa umarnin Gwamnan Yahaya Bello, na neman ya janye, shi kuma ya ce ba za ta sabu ba.

Sanata Smart Adeyemi ya yi zargin cewa tursasa wa daliget din aka yi cewa kada su zabe shi, sai ’yan kadan daga cikinsiu.

“An hana daliget daga wata karamar hukuma wadda Musulmi suka fi rinjaye su zabe ni, saboda baturen zaben, wanda dan karamar hukumar ce kuma Musulmi ne, ya umarce su da su zabi Sunday Karimi, wanda ya fito daga mazabar da ke makwabtaka da tawa.

“Karamar Hukumar ita ce Koton Karfe. Mako guda bayan zaben dan takarar, biyar daga cikinsu, dukkansu Musulmi suka zo Abuja, suka shaida min cewa Musulunci ya haramta musu cin hakkin wani,” inji shi.