✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanatoci na adawa da kara wa’adin dokat ta-baci

Galibin Majalisar Dattawa sun nuna rashin amincewa da bukatar Shugaban kasa ta kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da…

Galibin Majalisar Dattawa sun nuna rashin amincewa da bukatar Shugaban kasa ta kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Adamawa da Borno da Yobe.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya aike wa majalisar wasika yana neman ta amince masa ya kara wa’adin dokar da wata shida a karo na hudu, kamar yadda Shugaban Majalisar Sanata Dabid Mark ya karanta a ranar Talata.
Wasikar mai dauke da kwanan wata 17 ga Nuwamba, 2014, Shugaban kasar ya ce “Duk da kokarin da gwamnatinsa ke yi domin magance hare-haren ’yan ta’adda a jihohin, har yanzu ba a kawar da kalubalen tsaro da ya sa aka kafa dokar ba.”
Shugaban masu rinjaye a majalisar ya bude fage da cewa majalisar tana iya amfani da dokokinta don tattaunawa a kan wasikar, kuma lokacin da aka bukaci ra’ayin wakilan majalisar kan haka, sai sanatocin suka yi fatali da wannan bukata. Daga baya Sanata Mark ya roki sanatocin su tattauna a kanta inda ya ce koda ba za su amince da bukatar ba babu abin da zai hana su tattauna a kanta.
Nan take sai zauren majalisar ya kaure da surutu sanatocin suka shiga kamun kafa, lamarin da ya tilasta dage zamanta zuwa na sirri.
Galibin sanatocin da suka yi magana da manema labarai, sun nuna adawa da kara wa’adin dokar.
A ganawarsa da manema labarai Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) ya ce jihohin ba su bukatar kara wa’adin dokar ta-bacin. Ya ce Shugaban kasa yana da ikon tura sojoji su magance kowane hari a sashin kasar nan kamar yadda sashi na 218 na tsarin mulkin 1999 ya tanada ba tare da kafa dokar ta-baci ba.
A shekaranjiya Laraba Sanata Ahmad Lawan ya ce za su ci gaba da adawa da amincewa da dokar ta-bacin, inda ya ce, “Da dama muna adawa da ita; ni a kashin kaina ina matukar adawa da ita. Ina ganin ya wajaba mu nemo wasu hanyoyi na daban, amma wasu mutane suna tunanin wani abu daban. Amma za mu ci gaba da tattaunawa a gobe, (jiya Alhamis).”
Ya ce, ba a cika daya daga cikin ka’idoji takwas da suka bayar ba, domin amincewa da kara wa’adin dokar, “don haka ba na tsammanin za a samu wani bambanci idan muka sake bayar da wani sharadi a wannan karo.”
Sanata Kabiru Marafa (APC, Zamfara) ya ce ana kara samun zargi daga ’yan Najeriya cewa ba da gaske Gwamnatin Tarayya take yi ba wajen yaki da Boko Haram saboda ta ki ta kama tare da hukunta wadanda ake zargi da tallafa wa Boko Haram.
“dan Austireliya mai shiga tsakani Steben Dabis ya zargi Ali Sheriff da tsohon shugaban sojojin Najeriya Azubuike Ikejirika da hannu a lamarin Boko Haram, amma Gwamnatin Tarayya ta ki gabatar da su gaban shari’a, maimakon haka kwanakin baya sojoji sama da 200 karkashin wani Kanar suka rufa Sheriff baya zuwa Maiduguri. To mene ne amfanin kara wa’adin?”
Shi kuwa Sanata Kabiru Gaya (APC, Kano) cewa ya yi kafin kara dokar ta-bacin na baya “Babu karamar hukumar da ke hannun Boko Haram, amma yanzu kananan hukumomi 14 daga cikin 27 na Borno suna karkashin Boko Haram, to, kara wa dokar wata shida zai yi wani amfani?”
Sanata Sahabi Ya’u (PDP, Zamfara), kuwa cewa ya yi “muna cikin mawuyacin hali, saboda mun amince da kara ta har sau uku amma ba a cimma nasarar komai ba. Sai dai a lokaci guda ba za mu janye gaba daya ba. Me za mu kawo a madadin dokar ta-baci? Wannan shi ne tsaka mai wuya.”
A jiya Majalisar Dattawa ta ci gaba da tattaunawa kan batun, yayin da ta Wakilai ta fara zama a kan wasikar, kuma har zuwa hada wannan rahoto ba mu samu rahoton yadda lamarin ya kaya ba.