✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tunawa da Marigayi Abacha bayan shekaru 22

A ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2020 Marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekara 22 da rasuwa. Janar Sani Abacha  shi ne shugaban mulkin…

A ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2020 Marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekara 22 da rasuwa.

Janar Sani Abacha  shi ne shugaban mulkin sojin Najeriyasoji na 7. Ya kuma rasu ne a kan mulki a ranar 8 ga watan Yuni, 1998.

A ranar rasuwarsa ce kuma aka yi masa suttura aka binne shi a jihar Kano inda nan ne mahaifarsa.

Tarihin Abacha a takaice

An haifi Marigayi Abacha ne a Kano a ranar Litinin 20 ga watan Satumbar 1943.

Dan asalin jihar Borno ne da ya tashi a Kano ya kuma mayar da Kano ta zamo gida a gare shi.

Ya auri mai dakinsa Maryam Abacha ‘yar kabilar Shuwa Arab daga jihar Borno a shekarar 1965 wadda ta haifa masa ‘ya’ya maza 6, mata 3.

Yana kan mulki Maryam Abacha ta haifa masa dan autansa mai suna Mustapha a shekarar 1994.

Marigayi Sani Abacha shi ne Shugaban Kasar Najeriya na soji daya tilo da bai taba tsallaken mukamin soji ba har ya zama shugaban kasa mai mukamin Janar.

Farfado da tattalin arziki.

Duk da yadda wasu ke kallon mulkin sojin Marigayi Janar Abacha a matsayin mai tsauri tare da rashin sassauta wa bangaren kafafen yada labarai da fadin albarkacin baki, tsohon shugaban kasar ya kokarta wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma taka gagarumar rawa wurin alkinta asusun waje na Najeriya daga Dalar Amurka  miliyan 494 zuwa biliyan 9 da miliyan 600 a mulkinsa.

Gwamantin Abacha ta kuma biya kaso mafi yawa na bashin da ake bin Najeriya.

Ya kuma dakatar da matakin gwamnatocin baya na sayar da kadarorin gwamnati ga ’yan kasuwa, bisa hujjar cewa  ba a gina gwamnati domin cin riba ba, sai domin ’yan kasa su ci gajiyar ta.

Janar Sani Abacha ya rage hauhawar farashin kayan masarufi da kashi 54 bisa 100 domin saukaka wa talakawa radadin rayuwa.

Ya kuma yi nasarar yin haka ne a lokacin da farashin gangar man fetur yake Dalar Amurka 15 a kasuwannin duniya.

Babban ambaton a cikin gida

Babban aikin da aka fi ambaton Marigayi Abacha da shi shi ne kafa hukumar PTF.

Hukumar ta rika amfani da wani bangare na kudin da ya karu na litar mai tana gudanar da manyan ayyuka a faɗin kasar.

PTF ta yi fice wurin yin manyan ayyuka da samar da kaya masu matukar nagarta ga bangarori daban-daban a fadin Najeriya.

Ta rika samar da motoci da litattafai da gine gine da sauran kayan karatu kyauta a dukkan matakan ilimi.

Kuma gina manyan titunan da aka dade an cin moriyarsu a dukkan yankunan kasar.

Hukumar ta kuma bayar magunguna da kayan kul da marasa lafiya a asibitoci fadin kasar.

‘Kudaden Abacha’

Wani abu da ake ta cece-ku-ce a kai bayan rasuwar Marigayin shi ne zarginsa da boye kudade a kasashen Turai.

Irin wadannan kudaden ne gwamnatocin da suka biyo bayansa ke karbowa a lokaci zuwa lokaci domin aiwatar da wasu ayyukan ci gaban kasa.

Ko a baya-bayan nan ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbo irin wannan kudaden.

Wani abu da sunan Marigayi  yayi kauri a kai tun bayan mutuwarsa  shi ne batun kudin da ake cewa ta tara a kasashen Turai, kuma gwamnatocin da suka biyo sun yi ta kokarin karbo ire iren kudin.

Ko a kwanakin baya ma gwamnatin shugaba Buhari tayi nasarar karbo wani kaso na kudin da ake alaka ta wa da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha