Sanin Ubangiji | Aminiya

Sanin Ubangiji

    Fasto Enoch Atiyaye

Ya Ubangiji! Ka jarraba ni, Ka san ni. Ka sa duk abin da nake yi, tun daga can nesa ka gane dukkan tunanina. Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa, Ka san dukkan ayyukana. Tun kafin in yi magana Ka riga ka san abin da zan fada. Kana kewaye da ni a kowane sashe, Ka kiyaye ni da ikonKa. Yadda ka san ni ya fi karfin magana, Ya yi mini zurfi, ya fi karfin ganewata. Ina zan tafi in tsere wa ruhunKa? Ina zan gudu in tsere maKa? Idan na hau cikin samaniya Kana can, In na kwanta a Lahira Kana can, in na tashi sama, na tafi, na wuce gabas, Ko kuma na zauna a can yamma da nisa, Kana can domin Ka bi da ni, Kana can domin Ka taimake ni. Da na iya rokon duhu ya boye ni, Ko haske da yake kewaye da ni ya zama dare, amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare Ka, Dare kuwa haskensa kamar na rana ne. Duhu da haske, duk daya ne gare Ka.

Kai ne Ka halicci kowacce gaba ta jikina, Kai ne Ka harhada ni a cikin mahaifiyata. Ina yabonKa gama Kai abin tsoro ne, Duk abin da Ka yi sabo ne, mai ban mamaki. Da zuciya daya na san haka ne. Ka ga lokacin da kasusuwana suke siffatuwa, Sa’ar da kuma ake harhada su a hankali A cikin mahaifiyata, Lokacin da nake girma a asirce. Ka gan ni kafin a haife ni. Ka kididdige kwanakin da Ka kaddara mini, Duk an rubuta su a littafinKa, Tun kafin faruwar kowanensu. Ya Allah! TunaninKa suna da wuyar ganewa a gare ni, Ba su da iyaka! In na kirga su, za su fi tsabar yashi, Sa’ar da na farka, har yanzu ina tare da Kai. Ya Allah! Da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye! ’Yan ta-da-zaune-tsaye kuma sai su rabu da ni! Suna ambaton mugayen abubuwa a kanKa, Suna fadar mugayen abubuwa gaba da sunanKa. Ya Ubangiji! Ga yadda nake kin wadanda suke kinKa, Da yadda nake raina wadanda suke tayar maKa! Kiyayyar da nake yi musu ta kai intaha, Na dauke su, su abokan gabana ne. Jarraba ni, ya Allah! Ka san tunanina, Gwada ni, Ka gane damuwata. Ka bincika, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni, Ka bi da ni a madauwamiyar hanya.

Yabo domin alherinSa da ikonSa

Zan yi shelar girmanKa, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maKa godiya har abada abadin. Kowace rana zan yi maKa godiya, Zan yabe Ka har abada abadin. Ubangiji Mai girma ne, dole ne a fifita yabonSa, GirmanSa ya fi karfin ganewa. Za a yabi abin da Ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya-manyan ayyukanKa. Mutane za su yi magana a kan darajarKa da daukakarKa, Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanKa masu ban mamaki. Mutane za su yi magana a kan manya-manyan ayyukanKa, Ni kuwa zan yi shelar girmanKa. Za su ba da labarin girmanKa duka, Su kuma rera waka a kan alherinKa. Ubangiji Mai kauna ne, Mai jinkai, Mai jinkirin fushi, Cike da madauwamiyar kauna. Shi Mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin duk abin da Ya halitta. Ya Ubangiji! Talikanka duka za su yabe Ka, Jama’arKa kuma za su yi maKa godiya! Za su yi maganar darajar mulkinKa, Su ba da labarin ikonKa, Domin haka dukkan mutane za su san manyan ayyukanKa, Da kuma darajar daukakar mulkinKa. MulkinKa, madauwamin mulki ne, Sarki ne Kai har abada. Ubangiji, Yakan taimaki dukkan wadanda suke shan wahala, Yakan ta da wadanda aka wulakanta. Dukkan masu rai suna sa zuciya gare Shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata, Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatunsu duka. Ubangiji Mai adalci ne a abin da Yake yi duka, Mai jinkai ne a ayyukanSa duka. Yana kusa da dukkan wadanda suke kira gare Shi, Wadanda suke kiranSa da zuciya daya. Yakan biya bukatar dukkan wadanda suke tsoronSa, Yakan ji kukansu, Ya cece su. Yakan kiyaye dukkan wadanda suke kaunarSa, Amma zai hallaka mugaye duka. A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duk su yabi sunanSa mai tsarki har abada!

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubangiji, ya raina! Zan yabe Shi muddin raina. Zan rera waka ga Allahna dukkan kwanakina. Kada ka dogara ga shugabanni, Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba. Sa’ar da suka mutu sai su koma turbaya, A wannan rana dukan shirye-shiryensu sun kare. Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne Yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, Wanda Ya halicci sama da duniya da teku, Da dukan abin da yake cikinsu. Kullum Yakan cika alkawuransa. A yanke shari’arSa takan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kubutar da daurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arSa, adalai. Yakan kiyaye baki wadanda suke zaune a kasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukkan zamuna! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

(Zabura 139,145,146)