✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sa’o’i 72 gabanin zaben fidda gwani, APC ta gagara fitar da sakamakon tantance ‘yan takara

Alamu dai sun nuna cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da wanda yake so ya zama magajinsa.

Yayin da ya rage sa’o’i 72 gabanin zaben fidda gwani na ’yan takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar APC, har yanzu jam’iyyar ta kasa fitar da sakamakon tantance ’yan takarar da kwamitin jam’iyyar ya yi kwanan nan.

‘Yan takara 23 ne kwamitin tantancewar karkashin jagorancin tsohon Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ya tantance a katafaren otel din nan na Transcorp Hilton da ke Abuja a ranakun Litinin da Talatar da suka gabata.

Tun bayan kammala aikin tantancewar awanni 72 da suka gabata, ‘yan takarar da ma magoya bayansu sun shiga dar-dar saboda rashin bayyanar da sakamakon.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwamitin tantancewar ya karbi wani korafi da aka gabatar masa a kan jigo a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Korafin ya fito ne daga wani mai suna Sagir Mai Iyali, wanda ya ce shi dan APC ne a Jihar Kano, inda ya bukaci kwamitin kada ya tantance tsohon gwamnan Jihar Legas din bisa zargin gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) takardun bogi.

Da aka nemi jin ta bakinsa dangane da jinkirin da aka samu wajen bayyana sakamakon tantancewar, Shugaban kwamitin, Cif John Odigi-Oyegun, ya ce har yanzu suna ci gaba da aiki a kan rahotonsu, tare da ba da tabbacin cewa ‘yan kasa za su ji sakamakon idan sun kammala aikinsu.

Game da takamammen lokacin da za a fitar da sakamakon, Oyegun ya ce “Ban sani ba tukuna, ba mu kammala aikin a kan shi ba.”

Jam’iyyar APC dai ta shirya gudanar da zabenta na fidda gwanin takarar Shugaban Kasa ne tsakanin ranakun 6 da 7 da kuma 8 ga Yuni. Wannan dai na zuwa ne bayan jam’iyyar mai mulki na dage zaben fidda gwaninta har karo biyu.

Rahotanni sun nuna Hukumar zabe INEC ta kara lokacin a kan wa’adin 3 ga Yunin da tsayar ne don bai wa jam’iyya mai mulki damar gudanar da zaben fidda gwani na masu takarar Shugaban Kasa a karkashinta.

Alamu dai sun nuna cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da wanda yake so ya zama magajinsa. An fahimci hakan bayan da Buharin ya gayyaci daukacin gwamnoni APC inda ya gana da su a fadarsa da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata, duk da dai Buharin bai ambaci sunan kowa ba.

Shakka babu bayanin Buhari ya ta da kura a Jam’iyyar APC. Domin kuwa, bangaren Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, da na Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da kuma na tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi na ra’ayin cewa sun fi bangaren Tinubu samun tagomashi a wajen Buhari.

Daliget 2,340 ne ake sa ran za su yi zaben fidda gwanin yayin babban taron na APC muddin ‘yan jam’iyyar suka kasa cin ma yarjejeniyar tsayar da mutum guda daga cikinsu. Daliget uku-uku aka ciro daga kowace karamar hukuma a tsakanin kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin kasar nan.

Ya tabbata cewa gwamnonin APC na son a dauki wani ne daga cikinsu da zai gaji Buhari, kuma tuni sun yi zama sau biyu a Abuja suna kuma shirin yin na uku don ganin yadda za su cin ma wannan kudirin nasu.

Gwamnonin APC biyar ne suka shiga neman takarar Shugaban Kasa da suka hada da: Kayode Fayemi (Ekiti) da Yahaya Bello (Kogi) da Abubakar Badaru (Jigawa) da Dave Umahi (Ebonyi) sai kuma Ben Ayade (Kuros Riba).

A hannu guda, gwamnonin ne suka mamaye kananan kwamitin da za su ja ragamar shirya Babban Taron jam’iyyar wadanda aka kafa su a Larabar da ta gabata kamar yadda sanarwar da Sakataren Hulda da Jama’a na APC na Kasa ya fitar.

Sanarwar da Barista Felix Morka ya fitar ta nuna cewa, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, su ne za su kula da bangaren sufuri da masauki.

Sannan Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da na Zamfara, Bello Matawalle za su kasancew masu kula da tsare-tsare da wurin taro.

Haka kuma Gwamna Bello Masari na Jihar Katsina zai jagoranci karamin kwamitin dokoki, Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule kuma a matsayin wanda zai kula da fannin yada labarai da hulda da jama’a.

Bugu da kari, Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya jam’iyyar ta dora wa nauyin kula da bangaren kasafi, sannan Sanwo-Olu na Jihar Legas shi zai jagoranci kula da sha’anin kudi da zirga-zirga.

Sai kuma kula da bangaren tsarin zama da kawata wurin taro da sha’anin tsaro wanda aka dora wa Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun tare da takwaransa na Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Ba a kafa kwamitin daukaka kara ba:

Yayin da ‘yan takara da magoya bayansu ke dakon sakamakon tantancewar da jam’iyya ta yi wa ‘yan takarar Shugaban Kasa, har yanzu APC ba ta kafa kwamitin sauraren korafe-korafen da ka iya tasowa a sakamakon aikin tantance ‘yan takara da ya gudana ba.

Akan samu irin wannan kwamitin ne da zarar an kammala tantance ‘yan takara domin a saurari korafin duk wani dan takarar da yake ganin an yi ba daidai ba.

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa kan wannan batu, Sakataren Hulda da Jama’a na APC na Kasa, Barista Felix Morka, bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.

Babu bukatar ta da hankula, inji Lawan da Yarima da Okorocha

Sai dai wasu daga cikin ‘yan takarar da aka tattauna da su a ranar Larabar sun ce, babu bukatar ta da hankula kan batun.

Daya da cikin magoya bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce kwamitin na bukatar isasshen lokaci don shirya rahotonsa.

“Komai na tafiya kamar yadda jam’iyyar ta tsara. Ya kamata a kyale kwamitin ya kammala aikinsa sannan ya mika wa jam’iyya don daukar mataki na gaba,” inji shi.

Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce jinkirin da aka samu wajen kammala hada rahoton kwamitin ba abin ta da hankali ba ne.

A tattaunawar da aka yi da shi ta waya, Okorocha ya ce, “Daidai ne, a karshe dai rahoton zai fito, ba na tunanin za a fuskanci wata matsala duba da irin mutanen da kwamitin ya kunsa.

“Mutane ne masu kima wadanda suka san sha’anin siyasa da zabe yadda ya kamata. Don haka, babu abin ta da hankali.”

Har wa yau, daya daga cikin ‘yan takarar kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima ya ce, “Batu ne da ya shafi jam’iyya, suna kan hanya madaidaiciya, kokari suke yi na tabbatar da ba a samu a kurakurai ba.

“Kuma ai da sauran lokaci tun da babban taron sai Litinin zai kankama sannan ana iya fitar da samakon ko da Asabar. Ina da kwarin gwiwa ga kwamitin.”

Ismail Mudashir Da Saawua Terzungwe Da Bashir Isah