✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saraki ya taya Atiku murnar lashe zaben fitar da gwanin PDP

Ya kuma jinjina wa magoya bayansa kan gudunmawar da suka ba shi

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma daya daga cikin wadanda suka nemi takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Bukola Saraki, ya taya dan takarar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar murnar lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar.

A ranar Asabar ce dai Atiku ya lashe ya zama dan takarar PDP a zaben 2023 mai zuwa bayan ya kayar da su Sarakin da sauran ’yan takara, yayin zaben da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Saraki ya kuma gode wa dukkan abokansa da magoya bayansa a fadin kasar nan kan yadda suka ba da himma wajen samar da manufarsa ta kawo sauyi da ake kira: #RealSolutions da #FixNigeria!

Ya kara da cewa, “Yayin da muke shirin tunkarar babban zaben gaba, ina alfahari da cewa sakonmu na #RealSolutions da jagoranci na gari ya ratsa zukatan miliyoyin matasan Najeriya a fadin kasar nan.

“Yanzu, dole ne mu hada kan dukkan ’yan takararmu a fadin kasar nan don gyara tattalin arzikinmu, mu dakile matsalar rashin tsaro da kuma kawo karshen tsadar rayuwa,” inji shi.

Bukola Saraki ne dai ya zo na uku a zaben da kuri’a 70 a zaben fid da gwani na Shugaban Kasa na jam’iyyar, wanda ’yan takara 14 suka fafata a cikinsa.