✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja

Ya ce babu batun sulhu tsakanin Gwamnatin Neja da ’yan bindigar da ke addabar Jihar.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya ce sarakunan gargajiya a Jiharsa  na cikin masu gayyato ’yan bindiga daga kasashen waje suna shigowa suna tafka ta’asa a Jihar.

Ya bayyana damuwarsa cewa jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu na kawar da ayyukan ta’ddanci a jihar, amma bata-gari na gayyato miyagun  da ke shigowa Jihar ta iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin suna barna.

“Ba za mu saurara wa duk basaraken da muka samu da hannu ba a ciki. Mun kama ’yan bindiga da suka shigo daga Sudan da Mali da aka dauke su aiki ta kafashen sada zumunta,” inji Gwamnan.

Yayin ganawa ’yan jarida bayan ya ziyarci Shugaba Buhari, Gwamna Sani Bello ya ce ’yan bindiga da ake dauka ta kafafen sada zumunta na shigowa Neja ne daga jihohin Kaduna da Katsina da ke makwabtaka da ita.

Ya kara da cewa mafi yawancin ’yan bindigar da ke shigowa Najeriya ta Jamhuriyar Benin “Fulani ne da ba sa saurara wa kowa, hatata maganar iyayensu.”

Babu sulhu da ’yan bindiga

Don haka ya ce babu maganar sulhu tsakanin Gwamnatinsa da ’yan bindigar da ke tayar da zaune tsaye a Jihar Neja.

Ya ce Gwamnatin Jihar ta shure batun sulhu da ’yan bindigar ne sbaoda ba su da cika alkawari.

Ya ce a baya, ba da son ran gwamantin ba ta yi sulhu da su, amma abin ya shiriri ce ba tare da samun biyan bukata ba.

Gwamnan ya ziyarci Buhari ne domin bayyana masa irin matsalar tsaron da sauran matsalolin da ke addabar Jihar Neja, inda ya ce matsalar ’yan bindiga ce babbar damuwar Jihar a yanzu.

Karuwar hare-haren ’yan bindiga a kauyukan Neja

A baya-bayan nan hare-haren ’yan bindiga sun karu sosai a yankunan Jihar Neja.

A wani sabon hari da suka kai kauyen Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro, ’yan bindiga sun kashe wani jami’in dan sanda, suka raunta wani mutum sannan suka yi awon gaba da shanu masu yawan gaske.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa na ranar Laraba ya sa mazauna kauyen sun dimauce.

Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Suleiman Dauda Chukuba ya tabbatar wa Aminiya ta waya cewa an kai wa kauyen hari.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta Tarayya sau kawo wa Karamar Hukumar dauki daga hare-haren ’yan bindiga da ke kara yawaita a yankin.

A ranar Larabar dai wasu ’yan bindiga sun kai hari Karamar Hukumar Rafi inda suka yi garkuwa da mutum biyar a kauyen Rigo.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun, domin karin bayani amma ya ce zai waiwaye shi.

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton, muna kiran wayarsa amma ba ta shiga.