✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakuna za su iya magance matsalar tsaro — Buratai

Idan gwamnati ta ba su dama za a samu ci gaba ta fuskar tsaron kasa.

Jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Benin, Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya ce, idan aka bai wa sarakunan gargajiya dama za su taimaka wajen inganta tsaron kasa.

Buratai wanda ke zaman tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, ya ce Sarakunan za su inganta tsaro lura da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen hadin kan al’ummar kasa tare da ci gabanta.

Janar Buratai wanda ya samu wakilcin tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) ya bayyana haka ne, a garin Osogbo, Jihar Osun.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya halarci taron bikin karramawar da Kungiyar ’Yan Jarida (NUJ), ta yi wa Babban Basaraken Owu-Kuta, Oba Hammed Adekunle Oyelude Makama, inda ya ce basaraken ya kawo wa al’ummarsa ci gaba domin inganta rayuwarsu.

“Kamar yadda kake gani, wannan taro ya hada kabilu da dama ga ’yan Arewa sun halarta, ga Yarabawa ga kuma al’ummar Ibo da sauran kabilun kasar nan.

“A daya bangaren kuma ga sarakuna nan daga sassa daban-daban wannan alamu ne na hadin kan kasa, wannan basaraken mutum ne na kowa da kowa.

“Mutum ne wanda ba ya son kabilanci domin yana mu’amala da jama’a da dama, akwai ire-irensa da dama a cikin sarakunan gargajiya kuma idan gwamnati ta ba su dama za a samu ci gaba ta fuskar tsaron kasa da dunkulewarta a matsayin kasa daya,” inji shi.

A jawabin Oba Hammed Adekunle Makama ya bukaci ’yan jarida su sanya kishin kasa a ayyukansu, ya ce kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya shi ya fi alfanu maimakon a rarraba.

Ya ce idan ’yan jarida suka yi aikinsu cikin kwarewa da kishin kasa za a samu ci gaba mai amfani.

Oba Makama ya shaida wa Aminiya cewa, abin da ake bukata a wajen al’ummar kasa shi ne: so da kaunar juna tare da kiyaye doka da oda da kuma sada zumunta a yayin da ake bukatar kwatanta adalci daga wajen mahukunta ta yadda za a yi wa kowa adalci gwargwadon iko.

Kungiyar NUJ, Reshen Gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Osun (OSBS) ce ta karamma Oba Hammed Adekunle Makama da lambar girmamawa ta dindindin lura da irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’ummar Jihar da kasa baki daya.