✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakunan Kano da Gaya sun taya Abba Gida-Gida murnar lashe zabe

Sarakan biyu sun taya sabon zababben gwamnan na Kano murnar lashe zabe.

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya sun aike wa zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf sakon taya shi murnar lashe zaben Gwamnan da aka gudanar a jihar.

A cikin wasiku daban-daban  da suka aike wa sabon Gwamnan, Bayero ya ce mutane sun yi amfani da Dimokuradiyya wajen samar da zabin da suke so.

Sarkin Kano ya gode wa malamai da masu ruwa da tsaki a Jihar kan yadda suka dinga addu’ar gudanar da zabe lafiya.

Ya bukaci sabon Gwamnan da ya yi aiki da kowane bangare don samar da ayyukan ci gaba da kuma bunkasa tattalin arziki a Kano.

Ya yi addu’ar samun zaman lafiya a Kano da sauran sassan Najeriya, sannan ya yi addu’ar Allah ya ba shi ikon kammala wa’adin mulkinsa cikin nasara ta hanyar samar da abubuwan ci gaba.

A nasa bangaren, Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya da yake taya Abba murnar lashe zaben, ya ce yana da kwarin guiwar zababben Gwamnan zai samar da shugabanci na gari.

“A madadina da iyalaina da daukacin al’ummar Masarautar Gaya, ina mai bayyana farin cikina tare da taya ku murnar nasarar da kuka samu a zaben gwamnan Jihar Kano da aka yi.

“Muna da kwarin gwiwa cewar mai girma gwamna zai samar da ci gaba ga Kano da ma kasa baki daya, idan aka yi la’akari da kwarewa, dimbin gogewa, muna fatan ka yi mulki mai inganci.