✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarautar Zazzau: Ana zaman jiran tsammani, kwana takwas babu sabon sarki

Ana ta zaman jiran tsammani a Zariya bayan shafe tsawon kwana takwas da rasuwar tsohon sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ba tare da an nada…

Ana ta zaman jiran tsammani a Zariya bayan shafe tsawon kwana takwas da rasuwar tsohon sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ba tare da an nada wanda zai maye gurbinsa ba.

Wasu majiyoyi dai sun tabbatar da cewa kowanne lokaci daga yanzu za a iya bayyana sabon sarkin bayan kammala addu’ar kwana bakwai da rasuwar tsohon sarkin ranar Lahadi.

Yanzu dai hankula sun soma karkata ga gwamnatin jihar wacce take da wuka da nama kan tantance wanda zai hau karagar, bayan da rahotanni suka nuna tun a ranar Juma’a masu zabar sarki na masarautar sun mikawa gwamnatin jihar sunaye uku wadanda a ciki ake sa ran za ta zabi sabon sarkin.

Kusan dai a yanzu babu wani batu da ya fi jan hankulan al’ummar masarautar da ma na sauran jama’a kamar na wanda zai zama sabon sarki inda akasarinsu ke fatan ganin wanda suke so ya samu.

Har yanzu dai babu tabbas a kan wanda zai gaji marigayi Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu a asibitin sojoji dake Kaduna a ranar Lahadin makon jiya yana da shekaru 84 a duniya.

Rahotanni dai sun ce ana samun tururuwar mutane a gidan Yariman Zazzau Alhaji Munir Jafaru wanda daya ne daga cikin masu neman sarautar, gidan Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da na Alhaji Aminu Shehu Idris.

Kowannensu dai na zuwa ne domin yin fatan alheri tare da fatan gwaninsa ya samu.

Tarihi ya nuna a baya dai ba a cika samun irin wannan jinkirin wajen nada sabon sarkin ba a masarautar ta Zazzau, inda galibi a cikin mako daya da mutuwar sarkin ko ma kasa da haka ake nada sabo.

An sauya sunayen da masu zabar sarki suka mika’

To sai dai rahotanni na nuna cewa an sauya asalin sunayen da aka kaiwa gwamnatin jihar Kaduna tun da farko wanda ke dauke da sunan mutum ukun da masu zabar sarki suka aike da shi.

Yanzu haka dai ance an sake mika wani sabon jerin sunayen wanda ya kunshi sunan aminin gwamna Nasiru El-rufa’i, wato Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a ranar Lahadi.

Siyasa na neman shiga…’

A cewar wata majiya, tsame sunan Bamallin daga jerin wadanda masu zabar sarkin suka mika wa gwamnatin tun da farko bai yi wa gwamnan dadi ba, wanda hakan ne ya tilasta kara sunansa domin a ba gidan sarautar da ya fito na Mallawa damar su ma a fafata da su.

A cewar majiyar, “Bayan canza jerin sunayen, yanzu haka sunan Bamallin ne ma a sama.

“Gwamnan na fuskantar matsin lamba kan ya ba gidan Mallawa sarautar ne saboda rabonsu da hawanta an haura shekaru 100.

“Babu ko tantama yanzu lamarin baki daya siyasa ta shiga ciki, akwai masu neman biyan bukata da yawa.

“Ko da yake gwaman na kokarin zama a tsakiya, amma babu tabbas zai iya yin hakan a wannan lokacin, musamman kasancewar shima yan da tasa bukatar,” inji majiyar.

Kazalika, wata majiyar a fadar gwamnatin Kaduna ta ce gwamnatin ba ta ji dadin sunayen farkon ba sakamakon Iyan Zazzau, Alahji Bashir Aminu ne ya sami maki mafi yawa, wanda kuma suke zargin yana samun goyon baya daga wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.

‘Gwamna ne ke da wuka da nama’

A yanzu dai kallo ya koma sama saboda gwamna ne kadai yanzu ke da wuka da nama a hannunsa wajen tantance wanda zai zama sabon sarkin.

Wasu majiyoyi a fadar gwamnatin sun ce la’akari da abubuwan da suka faru a daren ranar Lahadi, yanzu gwamnan ne kadai ya san me zai faru.

A cewar majiyar, “Gwamnan ya tattauna da masu ruwa da tsaki daban-daban kuma yana duba abubuwa da dama, ciki har da abinda zai iya biyo baya in ya yi fatali da shawarar masu zabar sarkin.

“Yanzu shawara ta rage ta shi ya zabi wanda ya ke so,” inji majiyar.

To sai dai da aka tuntube shi kan lamarin, mai ba gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya ki cewa uffan kan lamarin.