✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sardauna: Ba rabo da gwani ba…

Shekaru 52  ke nan da ‘yan kudu, musamman ma mutanen shiyyar Kudu-maso Gabas, suka fitar da maitarsu a fili,  suka dakile Gwamnatin Sa Ahmadu Bello…

Shekaru 52  ke nan da ‘yan kudu, musamman ma mutanen shiyyar Kudu-maso Gabas, suka fitar da maitarsu a fili,  suka dakile Gwamnatin Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato,  daya daga cikin guda hudu da ke  fadin tarayyar Najeriya, da kuma ta tarayya, wacce Sa Abubakar Tafawa balewa ya jagoranta. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon siyasar bakar gaba da kiyayya da daukacin ‘yan siyasan Kudancin kasar nan suka  nuna wa ‘yan Arewan da suke kukan cewa sun hana su rawar gaban hantsi a fannin mulki, sun kuma hana  ruwansu gudu a fagen siyasa.

Ba wani abu ne ya kai ga haka ba kuwa illa tsabar hassada da ganin kyashin Arewa, wacce kwarewar shugabanninta bisa mulki da kuma gwanancewarsu wajen shimfida adalci da tsananin kamanta gaskiya suka bambanta jihar da sauran takwarorinta guda uku. Wadannan ne halayen da suka inganta matsayin Arewa cikin dan kankanen lokaci,  har ta yi kunnen doki da jihohin Kudancin da suka yi mata fintinkau a dukkan fannonin raya kasa;  kuma a bisansu ne magabatan farko,  kamar su Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa balewa, suka aza harsashin gina Najeriya. 

Da ma an ce wanda duk ya riga ka barci zai riga ka tashi. To mutanen Kudanci sun tsere wa ‘yan Arewa da shekaru fiye da hamsin a fannonin zamani, tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka kasar nan. Shi ya sa suke ganin cewa Jihar Arewa ba komai ba ce, domin jama’arta ba su da ilmi kamar takwarorinsu da ke jihohin Gabas da Yamma, saboda haka nan tilas ne su kasance kaskantattun da za a rika ja tamkar dabbobin da za a kai mayanka. 

To amma ba hakan al’amura suka kasance ba. Jihar Arewar da suka dauka gajerar kuka ce mai saukin hawa sai ga shi ta gagare su tankwarawa; ta buwaya a fagen siyasa da diplomasiyya; ta zame ‘yar lelen Turawan da suka fahimci cewa ita ce kadai za ta iya tsara kyakkyawar manufar da za ta kai ga samun ‘yancin kasar cikin lumana da kwanciyar hankali; sa’annan kuma ita ce ke da halaye da kamilallun shugabannin da za su ririta ‘yancin da  aka samu don kai wa ga ci gaba mai ma’ana, kuma cikin hanzari. To, tun kafin samun ‘yanci likkafar ‘yan Arewa da jam’iyyarsu ta NPC ke ta yin gaba-gaba, aka kuma samu sukunin doddora  su bisa muhimman mukamai a gwamnatin tarayya, suka kuma zamanto zakakurai a majalisar wakilai, sai yadda suke so za a tankwara al’amuran gudanar da gwamnati don nakaltar da suka yi wa siyasa da yadda ake sarrafa ta don biyan bukatar ‘yan Arewar da ke da rinjaye a cikin majalisar.

Amma duk da cewa mutanen Arewa ne ke rike da ragamar gwamnatin tarayya kafin samun ‘yanci, ‘yan Kudu sun mamaye Arewa; su  ne ke rike da muhiman mukamai a kamfanonin kasuwanci da manyan ma’aikatun gwamnatin Arewa, abin da ya kai sai da Sardauna Ahmadu Bello ya bullo da wata manufa ta danka ragamar jan Arewa a hannun ‘yan Arewa, wacce ake kira Northernisation Policy, don a tabbatar cewa kafin samun ‘yanci ‘yan Arewa ne ke sarrafa al’amuransu da kansu, ba‘yan Kudun da ke musu danniya, suna musu wani gani-gani ba. Wannan abu bai yi wa mutanen Jihar Gabashin Najeriya dadi ba, domin kuwa su ne manufar ta fi shafa, saboda a lokacin hatta masu wanke gyambo a asibitocin gruruwa da kauyukan Arewa, ba ma akawunnai da manyan jami’an gwamnati ba, duk mutanen can ne.

Ko a fannin siyasa ‘yan Kudu sun kasa yin galba akan ‘yan Arewa, domin ta yadda duk aka kada, aka kuma raya, ‘yan Arewar ne dai ke yin galba wajen kafa gwamnatin tarayya. ‘Yan Kudun sun nemi yin kawance da wasu ‘yan siyasar Jihar Arewa don a  rarraba kan ‘yan’yanta, amma hakan bai sa hakarsu ta cimma ruwa ba game da hankoronsu na ganin an karkasa Jihar Arewa gida-gida don su ji dadin farraka jama’arta. daukacin al’ummomin Arewa, sarakunansu da talakawansu duk sun nuna cikakken goyon baya da biyayya ga Sardauna Ahmadu Bello wanda ya kare musu mutunci, ya daukaka mtsayinsu, sa’annan kuma ya hade kawunan kabilun Arewa sama da 250 wuri guda, suka zame tamkar uwa daya, uba daya, ba wani bambancin addini ko na kabilanci.

Saudauna Ahmadu ya hana ‘yan Kudu kurdowa don karfafa rikice-rikicen addini da suka fara haddasawa a yankin don wargaza hadin kan Arewa, sa’annan ya wanzar da muhimman ayyukan ci gaba, kwatankwacin wadanda  jihohin Gabas da ta Yamma ke tinkaho sun yi a yankunansu, fiye ma da yadda suka tsara nasu. A takaice dai Sardauna ya mayar da yankin Arewa abar sha’awa; abar kwaikwayo; wurin zaman lumana da karuwar arziki; inda ‘yan Kudu suka yi ta tuttudowa, suna cin arziki ba tare da kyara ko wata tsangwama ba. Amma wannan bai sa sun gode Allah, sun hadiye bakar gabar da suke nuna wa al’ummar da suke amfana da ita ba.

Rashin samun damar da ‘yan Kudu ba su yi ne ba don mamaye Arewa ya haddasa bakar kiyayyar mutanen Arewa a zukatansu, har hakan ya yi sanadiyyar kisan gillar da suka yi wa Sa Ahmadu Bello, Firimiyan Jihar Arewa, kuma Shugaban Jam’iyyar NPC na kasa baki daya  da Mataimakinsa a siyasance, kuma Shugaban gwamnatin tarayya, Sa Abubakar Tafawa balewa da amininsu na siyasa, Clief Samuel Ladoke Akintola, Firemiyar Jihar Yamma, don dai a kawo karshen mulkin ‘yan Arewa a Najeriya. Wannan manufa ba ta yi tasiri ba, domin kuwa ta yi sanadiyyar yakin basasar da ya jawo hasarar miliyoyin rayukan ‘yan Najeriya.

Abin takaici game da haka shi ne  yadda zargin da ‘yan Kudu ke yi wa ‘yan Arewa  ya zame abin gaskatawa  a halin  yanzu, domin kuwa  suna cewa  shugabanni daga yankin ne mafiya yawa da suka ja ragamar Najeriya, amma sai ga shi nan yankin Arewa na ci gaba da kasancewa koma-baya, domin kuwa babu wani abin kirki ko na arziki da suka tsinana.  Ana iya gasgata haka a halin yanzu domin kuwa ‘yan Arewar da ke jan ragamar kasar sun fi mayar da hankali ga wani bangaren kasar, suka kuma  kawar da kai daga matsalolin da suke addabar yankin da ya bayar da zunzuruntun kuri’un da suka yi sanadiyyar hayewarsu bisa mulki.

A yanzu haka dai ana iya cewa wasu can daban  ne ke karkata akalar shugabannin Arewa suna aiwatar da wasu manufofi da kuma tsare-tsaren da nan gaba za su zamanti illa ko kuma marasa alfanu da alheri ga daukacin al’ummomin shiyyoyin Arewa, ba kamar yadda shugabannin Arewa na farko suka dage ba wajen hada kawunan dimbin al’ummar yankin, suka kuma samu nasarar habaka harkokin  tattalin arziki da na zamantakerwa  har hakan ya kai ga daukaka matsayin yankin cikin dan kankanin lokaci. Shi ya sa  jama’ar yankin Arewa ke tuna bara domin ba su ji dadin bana, suke kuma kukan cewa ba rabo da gwani ba, kamin a samu wani ne a makwafinsa.