✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Abdallah ya rantsar da sabuwar gwamnati

Sarki Abdallah na kasar Jordan ya rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasar

Sarki Abdallah na kasar Jordan ya rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasar da ke cikin matsi.

Yayin bikin da ya gudana a ranar Litinin, Sarkin ya umarci sabuwar gwamnatin karkashin Bisher al Khaswaneh ta hanzarta aiwatar sauye-sauyen da suka samu goyon bayan Asusun Lamuni na Duniya (IMF).

Jordan ta dauki matakin yi wa tattalin arzikinta garambawul ne da nufin farfado da shi daga matsi mafi tsanani da ya shiga sakamakon annobar coronavirus.

A ranar Laraba ne aka nada Khasawneh, mai shekara 51 domin ya maye gurbin Omar al Razzaz, a daidai lokacin da jama’ar kasar ke nuna bacin ransu game da kara tabarbarewar tattalin arziki.

Masu korafe-korafe a Jordan na kuma zargin gwamnati da tauye hakkin walwalar jama’a a karkashin sabbin dokokin da ta sanya da nufin dakile yaduwar cutar.