✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sarki Shehu Idris ya ba da gagarumar gudunmawa a Najeriya’

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Muhammad Namadi Sambo, ya yi addu’ar Allah Ya gafartar wa Sarkin Zazzau, marigayi Shehu Idris, Ya kuma sa Aljannah ce…

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Muhammad Namadi Sambo, ya yi addu’ar Allah Ya gafartar wa Sarkin Zazzau, marigayi Shehu Idris, Ya kuma sa Aljannah ce makomarsa.

A ziyarar ta’aziyyarsa ga Fadar Sarkin Zazzau, Namadi Sambo ya ce margiayin ya ba wa Najeriya babbar gudunmuwa.

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga Masarautar Zazzau da jama’ar garin Zariya da Jihar Kaduna da kuma Najeriya baki daya game da rasuwar Tsohon Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris.

Namadi ya kara da cewa, “Mun yi rashin uabin koyi Marigayi Dokta Shehu Idris.

“Zan iya  tunawa tun a shekarar 1986 marigayin yake ta ba da gudunmawa na tsawon lokaci. A lokacin da nake Kwamishina ya taimaka mana har zuwa wannan lokacin a jihar Kaduna da Najeriya.

“A yanzu haka addu’a za mu yi masa Allah Ya sa ya huta, Ya bai wa iyalansa hakurin rashin Sarkin Zazzau.

“Marigayi Shehu Idris ya ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba a yankin Zazzau da jihar Kaduna da kuma Najeriya”, kamar yadda ya bayyana.