✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki ya kaddamar da aikin lantarki daga hasken rana a Bichi

Akalla gidaje 12,000 ne ake sa ran za su amfana da shirin a masarautar.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki daga hasken rana mai karfin megawats takwas a garin Bichi ranar Asabar.

An kaddamar da aikin ne domin bunkasa harkar wutar lantarki a masarautar ta Bichi.

Akalla gidaje 12,000 ne a wurare kimanin 40 da ke Kananan Hukumomi tara na masarautar ake sa ran za su amfana da shirin.

Wani kamfani mai suna Sandstream ne dai zai gudanar da aikin tare da hadin gwiwar Hukumar Samar da Wutar Lantarki ga Yankunan Karkara ta Kasa (REA) don magance matsalar karancin wuta da kuma ba kasuwar hatsi ta Dawanau damar yin kafada da kafada da sauran takwarorinta na duniya.

Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin, shugaban kamfanin na Sandstream, Alhaji Ibrahim Abagana ya ce za su tabbatar da kammala aikin cikin nasara domin amfanin manoman yankin da kuma ’yan kasuwar Dawanau.

Shi kuwa Sarkin na Bichi, gode wa kamfanin da ma dukkan wadanda suka taka rawa wajen kawo aikin ya yi zuwa masarautar tasa.

Ya kuma ce tuni masarautar ta kafa wani kwakkwaran kwamiti da ya kunshi Hakimai da Dagattai domin tantance kauyukan da za su amfana da shirin.

Alhaji Nasiru Bayero ya kuma yi kira ga ’yan kasuwar Dawanau da su tabbatar da samun nasara da kuma dorewar aikin.