Sarkin Bichi ya shirya taron addu’o’i saboda matsalar tsaro | Aminiya

Sarkin Bichi ya shirya taron addu’o’i saboda matsalar tsaro

    Zahraddeen Yakubu Shuaibu, Kano da Abubakar Muhammad Usman

Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya shirya taron addu’o’i na neman agajin Allah kan matsalolin tsaro da suka addabar kasar nan musamman a Arewa.

An gudanar da taron addu’o’in ne a Babban Masallacin Juma’a na garin Bichi da ke Jihar Kano, wanda sarkin da hakimai da malamai da mazauna masarautar suka halarta.

Babban Limamin Masarautar, Khalifa Lawal Abubakar Bichi ne ya jagoranci zaman wanda aka bude da karatun Alkur’ani sannan aka yi addu’o’i masu yawa ga shugabanni da kasa baki daya.

Khalifa Bichi ya kuma yi addu’ar samun albarkar wannan lokaci na damina.

Babban Limamin ya kuma roki taimakon Allah Ya yi riko da hannaye wajen zaben shugabanni na gari da kuma tabbatar da aminci a yayin Zabe 2023.

“Muna bukatar mu tuba zuwa ga Allah da neman gafararsa, duk wadannan [matsaloli] suna faruwa ne sakamakon dabi’u da munanan ayyuka da muke yi, Allah Ya gafarta mana baki daya,” a cewar Babban Limamin.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala sallar Juma’a, Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, ya ce taron addu’ar ya zama wajibi duba da irin kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.

Ya kuma ce yayin da zaben 2023 ke gabatowa, akwai bukatar a rika gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da shugabanci na gari.

“Muna fuskantar manyan kalubale musamman na tsaro a kasar nan, don haka ya zama wajibi a shirya irin wadannan tarukan addu’o’in domin neman zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’ummarmu.”