Sarkin Daura ya sake auro budurwa mai shekara 22 | Aminiya

Sarkin Daura ya sake auro budurwa mai shekara 22

Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk
Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk
    Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya sake angwancewa da budurwa mai kimanin shekaru 22 mai suna A’isha Yahuza Gona.

Aminiya ta samu rahoto cewa auren an daura shi a garin Safana da ke Jihar Katsina.

Majiyarmu da ta nemi a sakaya sunanta daga garin na Safana inda aka dauro auren ta ce, da fara neman auren da yin komai an yi shi ne cikin sati guda.

Kazalika, an yi auren ne tamkar a asirce domin babu wani shagalin bikin da aka yi.

Ita dai A’isha, amaryar Sarki, ’ya ce ga Alhaji Yahuza Gona, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Safana a lokacin da aka taba yin zaben kananan hukumomi ba tare da jam’iyya ba.

Tuni dai amarya na dakin mijinta kamar yadda wata majiyar ta shaida mana.