✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Ya rasu yana da shekara 79.

Allah Ya yi wa Sarkin Dutse, Dokta Nuhu Muhammad Sunusi CON rasuwa a wannan Talatar.

Kwamishinan Ayyuka na Musamman a Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar da rasuwar sarkin.

Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79.

Sakatare na musamman ga marigayin, Wada Alhaji Dutse ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran yin jana’izar sarkin ne a ranar Laraba a Dutse.

Takaitaccen tarihin Sarki Nuhu

An haife marigayin a shekarar 1945 a kauyen Yargaba da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Dokta Sanusi ya yi karatu a Firamare ta Dutse daga shekarar 1952 zuwa 1956.

Bayan kammala karatunsa na firamare, ya samu takardar shaidar Ilimi ta Kasa (NCE) a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, sannan kuma ya yi digirin na daya da na biyu a fannin Kasuwanci na kasa da kasa a Jami’ar Ohio ta kasar Amurka.

Sannan ya samu takardar shaidar kammala Diploma ta PGD a fannin Tsare-Tsare da Nazari  daga Jami’ar Bradford ta Birtaniya.

Kazalika, Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri a Jihar Imo, ta ba Sarkin lambar yabo ta PhD a fannin Gudanarwa.

Ya samu gogewa sosai a fannin shawarwarin aikin gona da sarrafa masana’antu da kasuwanci bayan ya yi aiki na tsawon shekaru.

A zamanin mulkinsa, Masarautar Dutse ta kara bunkasa, inda ya mayar da garin na Dutse mai wadata wanda bai takaita iya arzikin al’ummarta ba, har ma da farfado da wayar da kan jama’a da matakinsu na ilimi.