✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Fika ya yaba wa ’yan jarida kan wanzar da zaman lafiya

Sarkin Fika, Muhammad Ibn Idrissa, ya yaba wa ’yan jaridan  bisa jajircewarsu wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaman lafiya a shiyar Arewa…

Sarkin Fika, Muhammad Ibn Idrissa, ya yaba wa ’yan jaridan  bisa jajircewarsu wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaman lafiya a shiyar Arewa maso Gabas.

Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe ya yi wannan jinjina ce a lokacin da kwamitin shirya gasar wasannin shekarar 2021 na jihar da Kungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) ta ziyarce shi a fadarsa da ke garin Fataskum.

Sarkin ya ce gudummawar da ’yan jarida suke bayarwa wajen samar da zaman lafiya a jihar Yobe da ma yankin Arewa maso Gabas abun a yaba musu ne.

“Muna son mu karfafa wa ’yan jarida gwiwa a lokacin rikice-rikice, sannan mu yaba muku da irin rawar da kuke takawa wajen ganin tsaro ya inganta a Jihar Yobe, kuna aiki tukuru don tabbatar da ganin zaman lafiya ya samu, shi ya sa muke jinjina muku bisa rahotaninku a tsakanin al’umma.”

Sarkin ya tabbatar musu da cikakken hadin kai da goyon bayansa kan wasan zaman lafiyan 2021 da NUJ/SWAN ta shirya inda ya ce hakan yana da muhimmanci, ganin yadda zaman lafiya yake kara samuwa a yankin na Arewa maso Gabas.

A jawabin sa, tun da farko, Shugaban SWAN reshen jihar Yobe wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya gasar, Kagana Amshi, ya shaida wa sarkin cewa tuni masu ruwa da tsaki suka shigo suka bada tasu gudummawa a wasan.