✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Funakaye da ke jihar Gombe ya rasu

Ya rasu ne sakamakon bugun zuciya

Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga rasuwa sakamakon bugun zuciya.

Sarkin na Funakaye, ya rasu ne a daren Asabar da misalin karfe 12:00 na dare.

Kafin rasuwarsa, marigayin ko a ranar Asabar ya halarci taron da Ministan Sadarwar, Isa Ali Ibrahim Pantami ya gudanar a Otel din Custodian da ke Gombe, kafin ya koma garin sa na Bajoga da misalin karfe 2:30 na rana

Marigayin ya zama Sarkin Funakaye ne bayan rasuwar yayansa, Alhaji Muhammad Kwairanga Abubakar, aka nada shi a ranar shida ga watan Fabarairun 2021, lokacin shi ne Dan Majen Funakaye

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na ranar Lahadi a fadarsa da ke garin Bajoga hedkwatar karamar hukumar ta Funakaye.