✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano Aminu: Bakon Shehu Maghili

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare masu muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce a kan…

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba, 2022 gwamnatin Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya dauki Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, zuwa kasar domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma auyukan shahararren malamin addinin Musulunci, sharifi kuma masanin falsafa, wato shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili, wanda ya yi rayuwarsa tun a karni na 15.

Jirgin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe.

A cikin wadanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano, Alhaji Ahmad Ado Bayero, Hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Danmalikin Kano da Dakta Ibrahim Dahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Dahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Hanyar Aljeriya

Jirgin ya dan yada zango a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda ya dauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan kasar Nijar da sauran malamai da mukaddamai da malaman jami’a.

Sarkin Kano da ’yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas, babban birnin Aljeriya, da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati da na diflomasiyya da kuma manyan malamai suka tarbi Mai Martaba Sarki da tawagarsa.

Daga nan aka yi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ’yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron kasa da kasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin Musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda ya yi rayuwarsa tun a karni na 15 kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare masu muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce a kan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar Yammacin Sudan.
Taron an shirya shi ne a babban dakin taro na kasar da ke birnin Aljiyes.

Rububin ganin Sarkin Kano

A ranar bude taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9:00 na safe amma sai aka kai shi wani daki ya zauna a kauwame har sai da dakin taron ya yi cikar kwari, sannan aka shigar da shi.
Toh dama an dauki makwanni ana ta yadawa a kafafen labarai cewa kasar ta Aljeriya za ta karbi bakuncin wani kasaitaccen sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Najeriya, don haka mutanen kasar duk sun zaku su ga wannan kasaitaccen sarki.

Saboda da haka yana shiga dakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guda, su kuma ’yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kada wa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An dauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai Martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daga nan ne kuma sai aka fara jawabai.

Babban Ministan Harkokin Addini na kasar shi ne ya wakilci shugaban kasa kuma ya yi jawabin maraba ga mahalarta taron kana ya yi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban kasa da al’ummar kasar baki daya.

Jawabin Sarki

Shi ma Sarkin na Kano ya yi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar kasar baki daya saboda kyakkyawar tarbar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar Masarautar Kano da Najeriya baki daya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan wadanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili, wanda ya ce ya fi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda dalilai da dama.

Ya bayyana wa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai wadanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili su ne ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shi ne Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a Majalisar Sarkin Kano.

A karshen jawabin Sarki ya yi godiya ga Allah wanda Ya kaddara cewa a zamaninsa ne aka yi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaka tsakanin Kano da Najeriya da kuma kasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfida.

Daga nan kuma sai aka bude fage inda malamai da masana suka yi ta kwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.
Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baki daga sauran kasashe kowa burinsa shi ne ya samu ya dauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota.

Mu ma ’yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ’yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa.

Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su dauki hoto da shi.

Bayan ya shiga daki kuma sai manyan malaman kasar su kuma suka yi layin shiga suna yi wa sarki addu’a har saida rana ta yi gora, sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

Liyafar ban girma

A rana ta biyu Mai Martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan an yi hutun zango na farko sai Mai Martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Najeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta tarbi Sarki da tawagarsa kuma an yi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shirya wa Mai Martaba Sarki wata liyafar alfarma a gidanta, inda aka gayyaci ’yan Najeriya mazauna kasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Najeriya.

A rana ta uku kuwa Mai Martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya kayatar kwarai, musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Liyafar shugaban kasa

Da yammaci kuma sai Shugaban Kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya gayyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma.

Shugaban kasar ya ce ya yi murna matuka da karbar bakuncin Sarkin, ya kara da cewa gwamnatin kasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunkasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Bakon Shehu Maghili

Shugaba Tebboune ya ce Sarkin Kano a wannan ziyara shi bakon Shehu Maghili ne, duk da ya yi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shi ne sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi, Sarki Aminu ya yi godiya ga Allah da Ya ba shi ikon amsa gayyatar shugaban kasar da kawo wannan ziyara.

Ya yaba wa gwamnatin kasar Aljeriya saboda dawainiyar daukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Farfado da hulɗar kasuwanci

Daga nan kuma sai ya yi kira ga shugaban na Aljeriya da su hadu su farfado da huldar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda ya ce zai taimaka wajen kara yaukaka dankon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu.

Tallafin karatu ga daliban Kano

Baya ga wannan kuma, da yake an ce lokacin iska ake cin dan jinjimi, sarkin ya bukaci gwamnatin kasar ta Aljeriya da ta ba wa daliban Jihar Kano tallafi na guraben kara ilmi a fannoni daban-daban a jami’oin kasar inda shugaban kasar nan take ya yi wuf, ya ce ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida, ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi, su kuma in Allah Ya so za su aiwatar.

A nan dai aka yi muwafuƙa duk shawarar ta su tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

Mahaifar Shehu Tijjani

A rana ta hudu Mai Martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ’yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa Darikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yi wa Sarkin da Kano da Nijeriya addu’oi na musamman.

Bankwana da Aljeriya

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida.

Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Najeriya su ne suka raka Mai Martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, aka yi bankwana kowa na cike da farin ciki.

Ribar ziyarar Sarkin Kano Aljeriya

Ko shakka babu wannan ziyara da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar kasar Aljeriya ta bude wani sabon babi na dangantaka mai karfi tsakanin kasar da kuma Njeriya.

Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda ya je lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai kaunar ci gaban Jihar Kano da Najeriya ba ki daya.

Dadin dadawa ga shi har Mai Martaba Sarki ya yi hobbasa har shugaban kasar na Aljeriya y ayi alkawarin bai wa daliban Jihar Kano guraben jaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na kara sanin makamar aiki.

Sannan a waje daya kuma shugaban na Aljeriya ya ba da umarni cewa a yi duk abin da za a yi don ganin kwance duk wani daurin gwarmai don sassauta huldar kasuwanci ga ’yan kasuwar Najeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai Martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taba samowa ba a bigiren dangantakar siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yi wa Allah godiya da muka samu sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.
Fatanmu shi ne Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar sama wa al’ummar Kano tudun dafawa, shi ma Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya dauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar ya yi nuni da cewa nan da dan lokaci zai gina wa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya Bakon Shehu Maghili !!!

 

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022