✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Sarkin Kano ya bukaci a daga darajar Rediyo Najeriya Kaduna

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira da gwamnati da masu hannu da shuni da su bayar da gudunmawa wurin bunkasa gidan rediyon…

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira da gwamnati da masu hannu da shuni da su bayar da gudunmawa wurin bunkasa gidan rediyon Najeriya Kaduna saboda muhimmancinsa ga Arewacin Najeriya da kasar baki daya.

Sarkin ya yi kiran ne yayin da yake karbar bakuncin tawagar hukumar gudanarwar gidan rediyon a fadarsa.

Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya ce tashar ta jima tana taimakawa wurin yada shirye-shiryen gwamnati da wayar da kan jama’a game da muhimmancin hadin kai, duk da karancin kayan aiki da take fama da shi.

Sarkin ya ce gidan Rediyo Najeriya Kaduna ya taka muhimmiyar rawa wurin hada kan al’ummomin Najeriya, baya ga samar da ingantattun labarai.

Basaraken ya yi kira da gwamnati, masu kudi, iyayan kasa, da daidaikun mutane su karfafi tashar ta hanyar samar mata da sabbin kayayyakin aiki na zamani don fuskantar kalubalen aikin jarida a wannan zamani.

Tunda farko Daraktan Gudanarwar gidan rediyon, Malam Buhari Auwalu ya ce sun kai wa ziyara Fadar Sarkin Kano ne don gaisuwa da neman tabarraki.

“Rediyo Kaduna na alfahari da kwararren mai yada labarai, mutumin Kano da ya jagoranci tashar tun wancan lokacin”, inji Buhari Auwalu.

Shi ma a nasa jawabin, Daraktan Shiyya na gidan radiyon, ya karfafi kiran na Masarautar Kanon ga al’umma su tallafa wurin farfadowa da inganta tashar don kara daga martabarta a idon duniya.