✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’a su hanzarta su yi rajistar katin zabe —Sarkin Kano

Mutanen Kudu sun fi na Arewa yawan wadanda suka mallaki katin zabe.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga jama’a wadanda ba su yi rajistar zabe ba da su hanzarta zuwa su yi.

Sarkin ya yi wannan kira ne a ranar Talata a wata sanarwa ta musamman da ya yi a fadarsa da ke birnin Dabo.

A sanarwar da aka watsa a ciki da wajen Jihar Kano, Sarkin ya jaddada muhimmancin yin rajistar katin zaben tare da ankarar da su kan illar akasin haka.

Ya yi kira ga wadanda na su ya bata, ko ya lalace, ko kuma a yanzu ne suka kai munzalin yin zabe, da su je su yi rajistar kafin a rufe.

Mai martaba sarkin ya yaba da irin kokarin da mutanen Kano suka yi a baya na fitowa su yi rajistar kwansu da kwarkwata, yana mai cewa a wannan karon ma kar su gajiya, wanda bai yi ba, ya je ya yi.

Wannan jawabi da kira na musamman ya zo ne a yayin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ke shirin rufe rajistar masu zabe a duk fadin kasar a ranar 31 ga watan Yuli.

Kiran na Sarkin Kano ya zo ne a daidai lokacin da alkaluma ke nuna yawan mutanen da suka yi rajistar zaben a Kudu, sun fi na Arewa, duk da cewa Arewa tana da rinjayen al’umma.

A baya, Hukumar INEC ta sa ranar kammala yin rijistar amma ta kara wa’adi sakamakon matsin lamba da kuma kiraye-kiraye na yin hakan daga jama’a.