✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya sabunta lasisinsa na tuki

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sabunta lasisinsa na tuki a wata ziyara da ya kai ofishin bayar lasisi na Jihar Kano.…

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sabunta lasisinsa na tuki a wata ziyara da ya kai ofishin bayar lasisi na Jihar Kano.

Sarkin na Kano ya kai ziyarar ce a ranar Litinin da misalin 10 na safe.

Sarkin ya isa ofishin hukumar ne da ke kan titin ‘Bank Road’ a jihar a inda manyan jami’an hukumar suka tarbe shi.

A hirar da Aminiya ta yi da wani wanda aka yi ziyarar a idonsa, ya ce Sarkin ya shiga cikin ofisishi a inda ya bukaci ya sabunta lasisinsa na tuki ne kamar yadda doka ta tanada.

A cewar majiyar, “an tarbi mai martaba Sarki an kuma yi masa abin da ya dace bisa doka, sannan suka rako shi ya fito ya tafi cikin girmamawa.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a kwanan baya ne tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya sabunta lasisin na tuki a ofishin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) da ke Abuja.