Daily Trust Aminiya - Sarkin Kano ya umarci jama’a su karbi allurar rigakafin coro
Subscribe

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero. (Twitter/@HrhBayero)

Sarkin Kano ya umarci jama’a su karbi allurar rigakafin coronavirus

Mai Martaba Sarkin Kano ya umarci al’ummarsa da su je a yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus da aka fara yi a Najeriya.

Sarkin Kano ya bayyana hakan ne yayain kiransa ga alumma da su ba da hadin kai ga yakin da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano suke yi da cutar.

“Su kuma jama’a ina umartar su karbi wannan rigakafin duk lokacin da aka samar da ita bisa shawarar masana,” inji shi.

Ya yi bayanin ne a fadarsa yayin da yake kira ga gwamnati da ta samar da allurar rigakafin cutar yadda zai wadaci al’umma.

Sarkin Kano ya ce, “A ’yan kwanan nan an nuna Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Mataimakinsa suna karbar allurar rigakafin wannan cuta.

“Muna kira ga mahukunta da su ci gaba da kokari don samar wa dukkan al’umma wannan rigakafi.”

Ya bayyana hakan ne yayin jawabin cikarsa shekara daya a kan Sarautar Kano ranar Talata 9 ga Maris, 2021.

A makon jiya ne dai Gwamnatin Tarayya da karbi rukunin farko na allurar rigakafin cutar, samfurin AstraZeneca guda miliyan 3.4 daga kasar Indiya.

A karshen makon jiya ne aka yi wa Shugaba Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Shguaban Maaikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari allurar.

More Stories