✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Karaye ya kai ziyara Masarautar Hadejia

Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar III ya kai ziyarar kwana daya Masarautar Hadejia, a Jihar Jigawa. Sarkin ya ce, dalilin ziyararsa Masarautar Hadeja…

Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar III ya kai ziyarar kwana daya Masarautar Hadejia, a Jihar Jigawa.

Sarkin ya ce, dalilin ziyararsa Masarautar Hadeja shi ne kyautata tsohuwar alaka da dangantaka mai dumbun tarihi da ke tsakanin Masarautar Hadejia da ta Karaye a Jihar Kano.

Sarkin Karayen ya roki Sarkin Hadeja da ya shige wa Manoman Masarautar Karaye gaba wurin Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Albarkatun Ruwan ta Tarayya da ta samar musu da hanyoyin ruwan da za su rika amfani da su wurin noman rani.

A nasa jawabin, Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje, ya yi tabbatar wa Masarautar Karaye cewa zai yi kokarin ganin sun amfana da aikin madatsar ruwa ta Hadejia-Jama’are.

Alhaji Adamu Abubakar Maje ya ce, shi da kansa zai tuntubi Ministan Albatun Ruwa a kan batun.

Sarkin na Hadeja wanda shi ne shugaban Majalisar Limamai da Sarakuna na Masarautun Jihar Jigawa, ya taya Sarkin na Karaye murnar zama sarkin yanka mai daraja ta daya, ya kuma gode masa bisa ziyarar wadda ya ce ba za a taba mantawa da ita ba.

Sarkin na Hadeja ya zaga da Sarkin na Karaye wasu wurare masu tsohon tarihi a masarautar da suka hada da Soron Yashi da ke Masarautar ta Hadejia.