✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmed ya mutu yana da shekaru 91

Kasar Kuwait a ranar Talata ta yi babban rashi bayan mutuwar Sarkinta, Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah. Sarkin wanda ya ci gajiyar gadon mulkin a hannun…

Kasar Kuwait a ranar Talata ta yi babban rashi bayan mutuwar Sarkinta, Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah.

Sarkin wanda ya ci gajiyar gadon mulkin a hannun dan uwansa, Sheikh Jaber al-Ahmed al-Sabah a shekarar 2006, ya yi gamo da ajali bayan shafe shekaru 91 a duniya.

Wani rahoto da jaridar BBC ta wallafa, yace ana saran kaninsa da suke uba daya, Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmed al-Sabah mai shekaru 83, ya maye gurbinsa.

A watan Yuli, aka kai Sheikh Saban wani asibitin Amurka sakamakon tiyatar da aka yi masa kan wata cuta da ba a bayyana ko mece ce ba.