✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kwatarkwashi a Jihar Zamfara ya rasu

Sarkin dai shi ne mafi dadewa a Jihar Zamfara

Basarake mafi dadewa a Jihar Zamfara, wanda ya shafe shekara 61 a matsayin Sarkin Kwatarkwashi da ke Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Umar (Mai-Kwatarshi), ya rasu.

Basaraken ya rasu ne ranar Alhamis, yana da shekara 93 a duniya.

A cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar, mai dauke da sa hannun Sakatarenta, Alhaji Kabiru Balarabe, ta ce Sarkin ya rasu ne bayan ya sha fama da doguwar jinya.

An dai yi jana’izarsa ce da misalin karfe 6:30 na yamma a fadarsa da ke garin na Kwatarkwashi .

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar III ne dai nada marigayin sarauta a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1961.

Marigayin dai ya shafe shekara 61 a kan karagar mulki.