✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya cika shekara 15 a kan mulki

A yanzu wasu na ganin cewa kamar ya fi sauran sarakunan da suka gabata.

A yau Talata, 2 ga watan Nuwambar 2021, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 15 a kan karagar mulki.

An nada Alhaji Sa’ad a matsayin Sarkin Musulmi a ranar 2 ga Nuwambar 2006, bayan rasuwar Sultan Muhammad Maccido wanda ke zaman yayan sarkin na yanzu.

A lokacin Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, Gwamnan Jihar Sakkwato na wancan zamani ne aka samu sabon sarkin wanda kuma shi ne ya jagoranci nadin Alhaji Sa’ad din a matsayin Sarki Musulmi na 20 a tarihin masarautar.

Sai dai a lokaci, an yi ta cece-kucen cewa ba lallai ya iya gudanar da sarautar kamar yadda sauran ’yan uwansa su ka gudanar ba, saboda kasancewar sa tsohon soja.

Sai dai kuma tun bayan hawan nasa, ya yi ba zata ganin yadda ya ke gudanar da mulkin ba kamar yadda ake tunani a baya ba.

Hasali ma, a yanzu wasu na ganin cewa kamar ya fi sauran sarakunan da suka gabata musamman wajen zama tare da talakawa da sauraron matsalolin da suka shafi al’umma.