✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau: Masu Zaben Sarki sun yi mubaya’a

Masu zabar sarki sun yi wa Sarki Ahmed Bamalli mubaya'a awanni kadan bayan an nada shi

Masu zabar Sarki na Masarautar Zazzau sun yi mubaya’a ga Sarki Ahmed Bamalli, ‘yan sa’o’i bayan an nada shi sarki na 19.

A ranar Laraba, 7 ga Oktoba ne aka nada Ahmed Nuhu Bamalli ya zama Sarkin Zazzau kwana 17 bayan rasuwar Sarki Shehu Idris wanda ya jagoranci masarautar tun daga 1975.

Bayan sanarwar nadin ne sabon sarkin cikin rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna ya isa fadarsa da ke Zariya, inda mabiya ke ta zuwa suna taya shi murna tare da mubaya’a.

Mubaya’ar ta su na zuwa ne jim kadan bayan daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar, Yariman Zazzau, Alhaji Munir Ja’afaru ya sanar da goyon bayansa ga nadin wanda ya ce haka Allah Ya so.

Masu zaben Sarki a Masarautar Zazzau sun hada da Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Fagacin Zazzau, Umar Mohammed; Makama Karami, Mahmood Abbas; Limamin Juma’a, Dalhat Kasim; da kuma Limamin Kona, Sani Aliyu.

Sarakunan Masarautar Zazzau na da gidajen sarauta hudu da suka hada da gidan Fulani, gidan Katsinawa, gidan Barebare, da gidan Mallawa.

Sarki Ahmed Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, wanda rabon gidan da hawa karagar mulkin masarautar ton shekarar 1920.

Shekara 100 ke nan rabon gidan da mulki tun bayan rasuwar Sarkin Zazzau na 13, Alu Dan Sidi — kakan Sarki mai ci daga gidan na Mallawa.