✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau ya kai wa El-Rufai ziyara

Sarki Ahmed Bamalli ya ziyarci Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai mako guda bayan nada shi

Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli, ya kai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ziyara ta farko ga Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.

Ziyarar da sarkin ya jagoranci ‘yan Majalisar Masarautar Zazzau na zuwa ne mako guda bayan Gwamnan ya nada shi Sarkin Zazzau na 19.

A ranar Laraba 7 ga Oktoba, 2020 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada Sarki Ahmed Bamalli bayan rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris sakamakon rashin lafiya.

Gwamna El-Rufai yayin karbar bakuncin Sarki Ahmed Nuhu Bamalli a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna
Wani sashe da ‘yan Majalisar Masarautar Zazzau da suka rako sarkin
Gwamna El-Rufai da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe da manyan jami’an gwamnatinsa a lokacin da suka karbi bakuncin Sarkin Zazzau.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo muku rahoto cewa daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar mulkin, Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu, ya shigar da kara yana kalubalantar nadin sarkin.

Iyan Zazzau wanda shi ne ya fi samun kuri’u daga cikin wadanda masu zabar sarki na masarautar suka zaba na bukatar kotu ta dakatar da ba wa Sarki Ahmed Sandar Mulki ta kuma ayyana sarautar da aka ba shi a matsayin haramtacce.

Karar da ya shigar a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna na bukatar a ayyana Alhaji Bashar Aminu a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19 kasancewarsa wanda ya fi samun kuri’u a zaben da aka yi.