✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Gyada (3)

A karshen makalar makon jiya na yi alkawarin farawa da bayanin wurare da dan kasuwa zai sayi gyada da yadda zai samu gyada a Najeriya…

A karshen makalar makon jiya na yi alkawarin farawa da bayanin wurare da dan kasuwa zai sayi gyada da yadda zai samu gyada a Najeriya da yadda zai sarrafa ta domin sayar wa al’ummar da ke kusa da shi da masana’antun gida Najeriya da kuma masu bukatar gyadar da albarkatunta a kasuwannin duniya.
Ita dai gyada an fi samun ta a garuruwa da kauyukan arewacin Najeriya da ke jihohin Sakkwato da Bauchi da Katsina da Zamfara da Nasarawa da Kaduna da kuma Kwara. Kodayake yanzu akwai sabon irin gyada da yake yalwa a jihohin yankin gabashin kasar nan, musamman ma jihohin Enugu da Anambra.
Ita gyada, sabanin ta da mafi yawancin albarkatun gona, ana samun ta a wadannan jihohi daga biranenta ya zuwa garuruwa da kauyukansu. Kuma sabanin farashin ba wani mai yawa ba ne, amma dan kasuwa na iya samun gyada a kan farashi mafi sauki a wasu kasuwanni da ake tara gyadar kwarai da gaske. Wadannan kasuwanni ba boye suke ba a jihohin arewa, ya danganta da inda dan kasuwa ke da zama. Misali, irin wadannan manyan kasuwa da ake tara gyada sun hada da danbatta a Jihar Kano da Garkin Daura da Mai’Aduwa da kankara a Jihar Katsina da Guru da Gaidam da Gashuwa a Jihar Yobe  da Maigatari a Jihar Jigawa da Talatar Mafara a Jihar Zamfara da dai sauransu.
Sayen gyada a wadannan kasuwanni na da dimbin alfanu fiye da farashi mai saukin da za a iya samu a kasuwannin. dan kasuwa zai iya samun irin gyadar da yake so a cikin wadannan kasuwannin da kuma iya yawan da yake bukata. Wanda ba ya harkar gyada zai ce ‘ashe gyada iri-iri ce?’ To gyada iri ce, kuma farashinta ya bambanta. Misali, akwai gyada ’yar Dakar, wacce kwayarta ta fi girma, ta fi jar fata, ta kuma fi mai, saboda haka ta kuma fi tsada. Hakan ya sa dan kasuwa zai je irin wadannan kasuwanni da irin gyadar da zai saya a cikin zuciyarsa.
A kuma irin wadannan kasuwanni dan kasuwa zai zabi gyada mai kyau ya saya domin zai same ta cike a kasuwa. dan kasuwa zai wuce zuwa ma’auna, inda zai zabi gyada ya saya, domin ita gyada ba kamar kowanne albarkatun gona ba ce, wacce za ka saya a gefen kasuwa, ko wajen ’yan tare da ’yan cori.
Farashin gyada yana kasancewa bai-daya a cikin kasuwa, sai dai yakan hau, ya sauka a rana daya daga lokaci ya zuwa lokaci. Wannan ya danganta da yawan gyadar da aka tara a kasuwa, a mafiyawan wasu lokutan kuma farashin na hawa ya sauka bisa yawan manyan kasuwanni da kuma yawan masu sayen gyada da suka halarci kasuwar.
Basirar sayen gyada a babbar kasuwa na kasancewa da irin bayanin da dan kasuwa ke da shi kafin ya fara ciniki a cikin kasuwar. Idan dan kasuwa bai taba cin kasuwar ba, sai ya yi kokari ya samu wanda ya san kasuwar, kuma ya yi huldar saye ko sayar da gyada a kasuwar a makon baya; ya kuma hakikance gaskiyar bayanin kasuwar zai samu daga gare shi. Abin da dan kasuwar zai nemi ya sani shine, a farashi nawa aka sayar da gyada a makon da ya gabata? Gyadar ta cika kasuwa, ko ba ta isa ba ana neman ta a makon baya? Mene ne girman mizanin kasuwar gyada a wannan kasuwar? Wannan tambaya ta karshe na nufin kimanin tan nawa na gyada ake tarawa a cikin ganiyar kakar gyada a wannan kasuwar?
Zan yi sharhi a kan wadannan tambayoyi domin fahimtar da dan kasuwa yadda zai sayi gyada a babbar kasuwa, domin samun ribar sarrafa ta, idan Allah Ya kai mu makon gobe. Idan kuma da sarari in yi wa dan kasuwa bayanin yadda zai sayi gyada a lokuta daban-daban na shekara, kafin kuma in kai ga yi masa bayanin yadda zai sarrafa gyada domin kasuwannin gida da na kasashen ketare.